Ainihin dalilin da yasa dan sanda ya harbe direba, Ado, jiya

Ainihin dalilin da yasa dan sanda ya harbe direba, Ado, jiya

Masu idanuwan shaida sun bayyana ainihin dalilin da yasa jami'in dan sanda ya bindige direban mota mai suna, Ado, a ranar Litinin yayinda ya nufi zuwa Abuja.

Daya daga cikin masu idon shaidan ya laburta cewa yan sandan na tsaye a kan titin Uso inda ya bukaci direban ya bada cin hanci amma ya ki saboda takardunsa sun cika kuma bai aikata wani laifi ba.

A cewarsa: "Yan sandan sun tsayar da shi kuma yayi biyayya. Sai suka bukaci kudi daga hannunsa amma yaki basu, ya bayyana musu cewa takardunsa sun cika. Daga baya suka fara ja-in-ja."

"Kawai sai dan sandan ya bindigeshi."

Kakakin hukumar yan sandan jihar Ondo, Femi Joseph, ya siffanta abinda dan sandan yayi a matsayin abin takaici.

DUBA NAN Taba sarkin Kano kaman taba yan Tijjaniyya ne gaba daya - Dahiru Bauchi ya gargadi Ganduje

Ya ce kwamishanan yan sandan jihar ya bada umurnin gudanar da bincike kan lamarin.

Yace: "Hukumar yan sandan jihar Ondo tana mai nuna takaicinta kan abinda ya kai ga mutuwar direban mota."

"Daya daga cikin jami'anmu ne ya harbeshi har lahira ne misalin karfe 1 na rana Uso."

"Kwamishanan yan sandan jihar Ondo ya bada umurnin kaddamar da bincike kan lamarin kuma za'a tabbatar da cewa dan sandan ya fuskanci fushin doka."

Kalli bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel