'Yar Buhari ta kammala digiri da sakamako mafi daraja daga jami'ar UK

'Yar Buhari ta kammala digiri da sakamako mafi daraja daga jami'ar UK

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi bikin murnar kammala digirin ‘yarta, Hanan, daga jami’a

- A wata sanarwar da Aisha Buhari ta yi a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa Hanan ta kammala ne da digiri mai darajar farko

- Uwargidan shugaban kasar ta mika godiyarta ga wadanda suka tallafawa ‘yarta wajen kammala aikinta na shekarar karshe

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta wallafa kyawawan hotunanta tare da Hanan Buhari a yayin murnar kammala digirinta na farko daga wata jami’a a UK. Rahoto ya nuna cewa, Hanan ta kammala ne da digiri mai daraja ta farko.

DUBA WANNAN: Saraki ya yi martani bayan kotu ta bayar da umurin kwace wasu kadarorinsa

A wallafar da tayi a shafinta, uwargidan shugaban kasar ta bayyana yadda ‘yan uwa da abokan arziki suka taya su murnar wannan nasarar. An yi bikin yaye ta ne a makarantar a yau Talata 3 ga watan Disamba.

Mahaifiyar cike da murna tare da tunkahon wannan nasarar, ta mika godiyarta ga jama’ar jihar Kebbi da suka hada da gwamnan jihar tare da uwargidansa a kan rawar da suka taka wajen aikin karshen da Hanan ta yi jami’ar.

Daga hotunan, Zahra Buhari da maigidanta duk sun hallara a wajen taron. An hango ‘yan uwa da abokan arziki duk a hotunan. Wacce ta kammala digirin, ta bayyana rike da shaidar kammala digirin a hannunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel