Taba sarkin Kano kaman taba yan Tijjaniyya ne gaba daya - Dahiru Bauchi ya gargadi Ganduje

Taba sarkin Kano kaman taba yan Tijjaniyya ne gaba daya - Dahiru Bauchi ya gargadi Ganduje

Shararren shehin malamin darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya aika sakon shawara da gargadi ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan kokarin dawo da masarautu hudu da kotu ta soke, BBC ta ruwaito.

Shehi ya bukaci Ganduje ya bar masarautar Kano yadda take a sakon muryan da ya aikawa BBC Hausa.

Dahitu Bauchi yace: ''Ina rokon Ganduje don Allah don Annabi ya bar batun nan kamar yadda kotu ta soke shi.''

"Ina jawo hankalinsa ya janye maganar nan, yadda kotu ta rushe wadannan abubuwa nasa, to ya hakura tun da ( kotu ta mayar) da Kano kamar yadda take shekara dubu da wani abu.''

"Ganduje ya kammala aikinsa cikin zaman lafiya, ya fi kan ya kammala ana tsine masa.''

"Taba fadar Kano taba mu ne gaba daya 'yan Tijjaniyya ne da masoyanmu.''

Taba sarkin Kano kaman taba yan Tijjaniyya ne gaba daya - Dahiru Bauchi ya gargadi Ganduje
Taba sarkin Kano kaman taba yan Tijjaniyya ne gaba daya - Dahiru Bauchi ya gargadi Ganduje
Asali: Facebook

Wannan ba shi bane karo na farko da Shehin Malamin zai nuna rashin jin dadinsa kan kafa masarautun ba.

Shehi ya ce da fatan gwamnan zai ji shawararsa kuma ya bar Kano ta zauna lafiya kamar yadda ya same ta.

Za ku tuna cewa kwamishanan yada labaran gwamnatin jihar Kano ya bayyana cewa majalisar zartarwar jihar ta yanke shawara a daren Lahadi cewa a sake gabatar da kudirin samar da sabbinn masarautu hudu majalisar dokokin jihar.

Kawo yanzu, yan majalisan sun amince da kudurin zagaye na farko kamar yadda ka'idar majalisa ta bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel