An kama wani tsohon kansila da laifin satar mota

An kama wani tsohon kansila da laifin satar mota

Tsohon kansilan karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, Samuel Adeojo ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa ta EFCC a kan laifin satar mota. Adeojo ya bayyana a matsayin shugaban kungiyar masu satar ababen hawa daga dilolin motoci.

Har zuwa yau Talata da aka kamashi, mai magana da yawun hukumar EFCC din, Wilson Uwujaren ya sanar da cewa, jami’ansu na ta bibiyar tsohon kansilan sakamakon korafe-korafen da ake kaiwa hukumar akan aiyukan kungiyarsu a jihar.

Hukumar ta ce, a kalla satar motoci uku aka danganta da wanda ake zargin kuma an samu dukkan ababen hawan a halin yanzu.

Takardar ta ce, "Kamar yadda binciken EFCC ya nuna, Adeojo na karyar shi likita ne inda yake bayyana suna daban-daban a matsayin nashi da kuma wuraren aiki daban-daban. Da hakan yake amfani wajen yaudarar mutane.”

DUBA WANNAN: Saraki ya yi martani bayan kotu ta bayar da umurin kwace wasu kadarorinsa

Kamar yadda hukumar ta sanar, daya daga cikin korafin satar da ta samu shine na wata mota kirar Toyota Avensis wagon, wanda Adeojo ya bayyana sunansa da Dr. Gboyega Omojola da ke aiki a asibitin koyarwa na Ibadan.

Tuni wani mai siyar da motoci mai suna Tunde Adejuwon, ya garzaya ya mika karar gaban hukumar EFCC a ranar 23 ga watan Maris. Ya bayyana yadda tsohon kansilan ya yi cinikin mota ta miliyan biyu a wajenshi. Tsohon kansilan ya ba direbansa na bogi cek din kudi don biya, amma sai daga baya aka gano bai biya ba. Kawai yayi amfani da hatimin bogi ne.

Mai siyar da motocin bai gano hakan ba har sai da suka tafi da motar. Irin hakan ce ta faru da wani Amos Onoja da ya kai karar kansilan.

An gano sa hannun tsohon kansilan a satar wata mota mai kirar Toyota matrix a Iwo, jihar Osun.

Hukumar EFCC din ta mika Oni zuwa gidan gyaran halin na Agodi, bayan umarnin da kotu ta bada na adana shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel