Masu zanga - zanga sun rufe hanyara Kaduna zuwa Abuja a kan sakamakon zaben kananan hukumomi

Masu zanga - zanga sun rufe hanyara Kaduna zuwa Abuja a kan sakamakon zaben kananan hukumomi

Jami'an 'yan sanda sun tarwatsa dandazon jama'ar da suka fito domin gudanar da zangar-zangar nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar a jihar Neja.

Dandazon fusatattun matasa sun fito zanga-zanga a kan babban titin Kaduna zuwa Abuja, lamarin da ya tilasta jami'an 'yan sanda harba musu barkonon tsohuwa tare da yin amfani da sanduna domin tarwatsa masu zanga - zangar.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa jami'an 'yan sandan da suka tarwatsa fusatattun matasa sun kama wakilinta duka sannan sun kwace na'urar mai nadar masa bidiyon yadda zanga-zangar ke gudana a yankin karamar Tafa.

Matasan sun rufe kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja kafin daga bisani jami'an 'yan sanda su fara harba bindiga a sama domin tarwatsa su.

Hukumar zabe ta soke sakamakon zaben karamar hukumar ne bayan an sace baturen zaben da ta tura yankin.

Shugaban hukumar zaben jihar Neja (SIEC), Aminu Baba, ya tabbatar da sace baturen zaben, amma dai bai bayyana sunan baturen zaben ba.

Sai dai, ya bayyana cewa baturen zaben malami ne da ke koyar wa a daya daga cikin manyan makarntun jihar.

Shugaban na hukumar SIEC ya kara da cewa basu san yadda aka sace baturen zaben ba, tare da sanar da cewa an sanar da su cewa ba a ga baturen zaben ba tun bayan kammala kada kuri'a a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel