Cikin watanni uku, bankunan Najeriya sun sallami ma'aikata 2,929

Cikin watanni uku, bankunan Najeriya sun sallami ma'aikata 2,929

Duk da cewa gwamnatin tarayya na cigaba da yiwa yan Najeriya alkawarin cewa za ta rage rashin aikin yi a Najeriya, bankunan ajiyan kudi a Najeriya sun sallami ma'aikata 2,929 tsakanin watan Yuli da Satumban 2019, rahoton ma'aikatar lissafi NBS ya bayyana haka.

Bayanan haka na kunshe cikin rahoton ayyukan bankuna wanda ya hada da kudaden da aka shigar, kudaden da suka fita da yawan ma'aikatansu.

A cewar rahoton, yawan ma'aikatan bankuna ya ragu kimanin dubu uku cikin kankanin lokacin inda jimillan ma'aikatan bankunan Najeriya ya tsaya a 101, 435 sabanin 104,364 a watanni uku da sua gabata.

Hakan na nuna cewa yan Najeriya dubu uku sun kan titi yanzu babu aikin yi kuma da yiwuwan masu iyali ne.

Rahoton ya kara da cewa yan Najeriya sun yi cinikayya ta hanyar wayoyi ko yanar gizo sau milyan dari takwas (800,201,498) na kudi N42.76 trillion tsakanin watan Yuli da Satumba.

DUBA NAN Rufe boda: Mun gano daruruwan gidajen mai a Magama Jibiya - FG

A bangare guda, Gwamnatin tarayya ta yi bayanin dalilin da yasa har yanzu ba'a biya ma'aikatan N-Power a fadin kasa kudin albashinsu ba na watanni biyu.

Shirin N-Power wani shiri ne da gwamnatin Buhari ta shirya domin rage yawan matasa maras aikin yi a fadin tarayya.

A cewar ministar walwal da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Farouq, an samu jinkiri ne saboda ba'a kammala mika ragamar aiki daga ofishin mataimakin shugaban kasa zuwa sabuwar ma'aikatar ba. Hakazalika ba'a sallami wadanda wa'adinsu ya kare ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel