Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya tashi daga Daura, ya tsaya a garin Kaduna

Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya tashi daga Daura, ya tsaya a garin Kaduna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammla iya kwanakin daya diban ma kansa zai yi a garin Dauran jahar Katsina, inda ya sauka a garin Kaduna domin halartar taron babban hafsan Sojan kasa na shekara shekara.

Da misalin karfe 9:42 na safiyar Talata, 3 ga watan Disamba ne jirgin shugaba Buhari ya tashi daga garin Daura bayan kammala zaman kwanaki 5 da ya yi a garin, inda ya sanya tubalin gina sabuwar jami’ar sufuri ta gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Da kyar na sha: Yansanda sun kubutar da budurwa yar NYSC daga hannun masu garkuwa da mutane

Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya tashi daga Daura, ya tsaya a garin Kaduna

Buhari
Source: Twitter

Jama’a da dama ne suka yi sallama da shugaban kasa yayin da jirgin nasa ya tashi, inda ya nufi garin Katsina, daga nan kuma ya tashi ya kama hanyarsa zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai jirgin shugaban ya yada zango a garin Kaduna domin ya halarci taron babban hafsan Sojan kasa, laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai da aka saba yi shekara shekara, inda gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai ya tarbe shi, kuma ya kai tsaye ya wuce da shi zuwa fadar gwamnatin jahar Kaduna.

Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya tashi daga Daura, ya tsaya a garin Kaduna

Buhari
Source: Twitter

Daga fadar gwamnatin jahar Kaduna ne kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamna El-Rufai suka karasa wajen taron babban hafsan sojan kasan, inda suka samu tarba daga wajen laftanar janar Tukur Yusuf Buratai.

A shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twittr, gwamnan Kaduna ya bayyana cewa Buratai yace ayayin ziyarar, shugaban kasa Buhari zai kaddamar da bude sabuwar asibitin Sojoji na 44 Nigerian Army Reference Hospital.

Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya tashi daga Daura, ya tsaya a garin Kaduna

Buhari
Source: Facebook

Haka zalika shi ma Buratai ya jinjina ma gwamnan jahar Kaduna bisa namijin kokarin da yake yi wajen tabbatar da tsaro a jahar Kaduna, da kuma manyan ayyukan more rayuwa da gwamnatinsa take gudanarwa.

Da dumi dumi: Shugaba Buhari ya tashi daga Daura, ya tsaya a garin Kaduna

Buhari
Source: Facebook

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel