Da kyar na sha: Yansanda sun kubutar da budurwa yar NYSC daga hannun masu garkuwa da mutane

Da kyar na sha: Yansanda sun kubutar da budurwa yar NYSC daga hannun masu garkuwa da mutane

Jami’an rundunar Yansandan jahar Legas sun sanar da ceto wata budurwa yar bautan kasa mai suna Faith Onyiwara da miyagun yan bindiga suka yi awon gaba da ita a yankin Illamija na unguwar Epe a jahar Legas.

Jaridar Punch ta ruwaito miyagun sun sace Faith ne a daidai lokacin da take kan hanyarta na zuwa taron mako mako nay an NYSC a lokacin da suka kamata, tare da saceta a karkashin jagorancin shugabansu mai suna Moses Ofeye.

KU KARANTA: Mayakan IPOB sun kashe mataimakin kwamishinan Yansanda, da kwamandan SARS, sun banka ma motarsu wuta a jahar Anambra

Da kyar na sha: Yansanda sun kubutar da budurwa yar NYSC daga hannun masu garkuwa da mutane
Faith
Source: Facebook

Kaakakin Yansandan jahar Legas, Bala Elkana ya bayyana cewa bayan sun dauketa, masu garkuwa sun nemi manajan gonar da budurwar take aiki a ciki dasu biya zunzurutun kudin fansa naira miliyan 50 kafin su sake ta.

Sai dai kaakakin yace babu wanda ya biya ko sisi wajen ceto Faith, ya kara da cewa sun samu nasarar cetota ne sakamakon wani samame da kwamshinan Yansandan jahar Hakeem Odumosu ya jagoranta a dajin Ilamija bayan inda aka yi musayar wuta tsakaninsu da miyagun.

“Kwamishinan Yansanda Hakeem Odumosu ne ya jagoranci aikin ceto Faith da misalin karfe 2:20 na daren Talata, Yansanda sun samu nasarar harbin shugaban yan bindigan Mosese Ofeye, kuma a yanzu haka yana hannu.

“A yanzu dai an garzaya da Faith zuwa asibiti domin samun kulawa biyo bayan tashin hankalin da ta yi fama da shi, sa’annan an mikata ga shugaban NYSC na jahar Legas tare da iyayenta.” Inji shi.

A wani labari kuma, tsagerun mayakan haramtacciyar kungiyar rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB sun kaddamar da wani hari a kan ayarin jami’an Yansandan Najeriya, inda suka kashe Yansanda biyu tare da banka ma motar Yansandan wuta a jahar Anambra.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel