Ajali ya yi kira: Yan mata 6 sun mutu a sanadiyyar hatsarin kwale kwale a Kebbi

Ajali ya yi kira: Yan mata 6 sun mutu a sanadiyyar hatsarin kwale kwale a Kebbi

Wani mummunan hatsarin kwale kwale ya rutsa da wasu yan mata guda shida a cikin wani ruwa dake karamar hukumar Suru ta jahar Kebbi, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban karamar hukumar, Alhaji Umaru Maigandi ya tabbatar da aukuwar hatsarin a ranar Talata, 3 ga watan Disamba, inda yace jirgin ya kifa ne a lokacin da yake tafiya a cikin rafin Tindafi domin tsallakawa dasu a ranar Litinin.

KU KARANTA: Mayakan IPOB sun kashe mataimakin kwamishinan Yansanda, da kwamandan SARS, sun banka ma motarsu wuta a jahar Anambra

A cewarsa, kwale kwalen ya tashi daga kauyen Tindifai dauke da yan mata guda 9 da zai kaisu Fadama inda zasu tafi domin aikin girbin shinkafa, amma a yayin da yake tafiya kwatsam sai ya kifa.

“A dalilin wannan hatsari yan mata 6 suka mutu, wanda shekarunsu basu wuce 12-15 ba, amma an samu nasarar ceto sauran yan matan guda 3, kuma matukin kwale kwalen ne ya cetosu, yaro dan shekara 13 mai suna Umar Faruk.

“Tuni aka gudanar da jana’izar yan matan kamar yadda Musulunci ya tanadar, kuma mun jajanta ma iyalansu, tare da tausaya ma wadanda suka tsallake rijiya da baya.” Inji Ciyaman Maigari.

Sai dai shugaban ya danganta lamarin ga daura adadin mutanen da suka fi karfin kwale kwalen sakamakon an yi kwale kwalen ne domin daukan mutane 5, amma aka sanya mutane 9 a cikinsa.

Haka zalika shugaban yace zasu cigaba da wayar da kawunan jama’an yankin game da hadarin dake tattare da cika mutane da kaya a cikin kwale kwale.

A wani labari kuma, tsagerun mayakan haramtacciyar kungiyar rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB sun kaddamar da wani hari a kan ayarin jami’an Yansandan Najeriya, inda suka kashe Yansanda biyu tare da banka ma motar Yansandan wuta a jahar Anambra.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel