Ba lallai PDP ta shiga zabukan da za a gudanar nan gaba ba - Secondus

Ba lallai PDP ta shiga zabukan da za a gudanar nan gaba ba - Secondus

Jam'iyyar PDP, babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, ta bayyana tsoronta na kara fitowa zaben takarar kujerar gwamnonin jihar Edo da Ondo da za a yi a cikin shekarar 2020 mai zuwa.

Jam'iyyar ta kara da bayyana bacin ranta a kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa.

A don haka ne jam'iyyar PDP din ta dora nauyin kawo gyara a lamurran zabe a kan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, wajen shawo kan kalubalen magudin zabe da ya gallabi kasar nan.

Shugaban jam'iyyar PDP ta kasa, Prince Uche Secondus ne ya sanar da hakan yayin jawabi ga waklin INEC wanda ya je tantancer jam'iyyar a babban ofishinta da ke Abuja.

A yayin jawabi ga wasu jami'an hukumar zaben, Second us ya zargi cewa, nagartar hukumar na cikin barazana ganin yadda aka yi zabe a kasar nan.

Ya bayyana yadda wasu jami'an hukumar INEC din suka lalata jiga-jigan dokokin hukumar.

A kalamansa, "A halin yanzu, nagartar INEC a bar tantama ce. Wasu daga cikin jami'an hukumar sun tozarta kujerunsu.

"Muna shawartar INEC da ta koma don sake shiri tare da duban sauran zabukan da ake yi s kasar nan.

"Ko INEC na bukatar gyare-gyare. Ba zai yuwu mu cigaba a haka ba. Kodai mu zabi salon Amurka ko na kasar Egypt wajen yin zabe, inda sojin kasar ke shiga lamurran zabe tsundum."

Shugaban jam'iyyar PDP din ya kara da bayyana cewa, lokaci ya yi da INEC din zata mika bukatar kawo gyara ga wasu dokokin zaben a gaban majalisar dattawan ta yadda za a samu cigaba a bangaren zabe mai nagarta.

Ya kara da cewa, yadda aka yi zaben 2019 ya maida Najeriya baya be kawai.

DUBA WANNAN: Bayan samun nasara a zabe: Yahaya Bello ya sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa a Kogi

Kadan daga cikin miyagun darussan da aka koya a zaben sun hada da: daba, kisan kai, tarwatsa wajen zabe, da sauransu.

Sauran sun hada da, zargin INEC da ake da hannu wajen cimma burin APC, firgita masu zabe, canza sakamako, kwace kayayyakin zabe, tura jiragen yakin soji don tsoratar da jama'a.

A mayar da matanin mataimakin daraktan INEC din, Musa Husunu ya ce za a kiyaye wadannan kararrakin na PDP.

Husunu ya bayyana makasudin zuwansu ofishin shine, tantancewa wanda ya hada da shaidar ofishin ne hedkwatar INEC, kwafi biyar na kundin tsarin mulkin jam'iyyar, jerin sunayen shuwagabannin jam'iyyar, shaidar rijistar mambobi da kuma bayanin asusun bankinsu.

Amma PDP ta ce, lamarin da ya fara a Osun, Ekkti, Bayelsa da Kogi ba damokaradiyya bane. Kuma su ne zasu iya hana jam'iyyar fitowa sauran zabukan siyasa nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel