Mun bankado yunkurin hargitsa Najeriya - DSS

Mun bankado yunkurin hargitsa Najeriya - DSS

A ranar Talata ne hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana cewa ta bankado yunkurin wasu kungiyoyi na tayar da tsugune a sassan Najeriya da kuma babban birnin tarayya, Abuja.

A cikin wani da jawabi da jami'in hulda da jama'a a hukumar DSS, Dakta Peter Afunanya, ya fitar a Abuja, ya ce akwai yunkurin ingiza wutar zanga-zanga da bore da tayar da zaune tsaye domin a kawo hargitsi a cikin kasa.

"Masu yunkurin kawo hargitsin sun yi niyyar fara wata babbar zanga-zanga da a dukkan sassan Najeriya, musamman a manyan birane kowanne yanki, a cikin 'yan makonni kalilan masu zuwa. Sun zabi irin wannan lokacin ne saboda yawan bukukuwan da ake gudanar wa a karshe da farkon shekara.

"Saboda sanin matsalolin da hakan kan iya haifar wa ne yasa hukumar DSS ke son aika sakon gargadi ga wadannan kungiyoyi makiya dimokradiyya da su sani cewar zasu fuskanci fushin hukuma matukar basu janye mugun nufinsu ba.

DUBA WANNAN: Bayan samun nasara a zabe: Yahaya Bello ya sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa a Kogi

"A saboda haka muke yin kira ga iyayen yara da su gargadi 'yayansu a kan shiga irin wadannan kungiyoyi da kuma amfani da su wajen tayar da hankalin sauran 'yan kasa masu kaunar zaman lafiya. Muna kara yin wani kiran ga shugabannin makarantu da su gargadi dalibansu da ma'aikatansu daga shiga cikin duk wata sabga da kan iya kawo hargitsi a cikin kasa," a cewar jawabin.

Jawabin ya kara da cewa rundunar DSS da sauran hukumomin tsaro zasu kasance cikin shiri a dukkan sassan Najeriya domin tabbatar da tsaron lafiyar al'aumma da dukiyoyinsu da kuma dakile tare da daukan mataki a kan duk wani yunkurin kawo hargitsi a cikin kasa.

Kazalika, hukumar DSS ta yi kira ga sauran 'yan kasa masu kaunar zaman lafiya da kar wani abu ya firgita su ko ya hana su fita domin gudanar ta harkokinsu na yau da kullum tare da basu tabbacin cewa jami'an tsaro zasu kasance a kowanne lungu da sako domin tabbatar da cewa komai ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel