Samun matsalar 'amsa kuwwa' ya haifar da rudani a zauren majalisar dattijai

Samun matsalar 'amsa kuwwa' ya haifar da rudani a zauren majalisar dattijai

A ranar Talata ne majalisar dattawan Najeriya ta hargitse bayan shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, ya kasa jawabi ga majalisar sakamakon lalacewar amsa kuwwar majalisar.

Sanata Abdullahi ya yi kokarin jawabi ne a kan mutuwar dan majalisar da ya rasu, Hon. Jafaru Illiyasu Auna, wanda ya rasu a Abuja a ranar Lahadi.

Jafaru Iliyasu dan majalisa ne mai wakiltar Rijau/Magama a majalisar tarayya, kafin rasuwarshi.

Kokarin 'yan majalisar na gyara amsa kuwwar ya tashi a tutar babu.

Bayan kasa amfani da amsa kuwwar mazauninsa, shugaban majalisar dattawan ya amincewa sanatan da ya yi magana da amsa kuwwar wani mazaunin, wanda hakan ya yi karantsaye ga dokar majalisar.

"Shugaba, kaine shugaban majalisar, zaka iya magana a ko ina," Lawan ya ce.

Kamar yadda sashi na 11, sakin layi na 2 na dokar tsayuwa na majalisar a 2015, "Sanata zai iya yin magana ne a mazauninsa kadai, matukar shugaban majalisar dattawan zai iya sauya mishi lokaci zuwa lokaci."

Bayan maganar da shugaban majalisar dattawan yayi, shugaban majalisar ya koma mazaunin sanata Jibrin Barau inda ya mika bukatar ga majalisar.

DUBA WANNAN: Bayan samun nasara a zabe: Yahaya Bello ya sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa a Kogi

A wannan halin kuma, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan, Enyinnaya Abaribe, ya kasa amfani da amsa kuwwar da ke mazauninsa.

Abaribe ya garzaya zuwa mazaunin Barau wanda ke gefen mazaunin shugaban masu rinjayen majalisar, don goyawa bukatar baya.

Wannan tashin da Abaribe yayi, ya jawo ihu tare da sowa daga sanatocin jam'iyyar APC a majalisar. Sun hana shi canza mazauni don samun amsa kuwwar da zai goyi bayan bukatar shugaban masu rinjayen.

A daukin da Lawan ya kai, yace "Yau din nan ba kamar kullum bane, idan shugaban marasa rinjayen ya zauna a mazaunin da ba nashi ba, yanayi ne ya bukaci hakan ne."

Kafin goyon bayan bukatar, Abaribe yace: "amfanin da nayi da amsa kuwwar Jibrin Barau na bayyana mana cewa akwai bukatar gyaran majalisar nan."

Idan zamu tuna a wani makon, Lawan ya zargi cewa zafin majalisar ya tsananta saboda yadda na'urorin saukar da raba na majalisar basa aiki.

Majalisar ta dage cigaba da zama har zuwa ranar Laraba bayan da aka yi shirun minti daya don karrama marigayi Hon. Auna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel