Mamba a majalisar wakilai daga arewa ya kara rasuwa a cikin kasa da sa'a 24 da mutuwar Iliyasu

Mamba a majalisar wakilai daga arewa ya kara rasuwa a cikin kasa da sa'a 24 da mutuwar Iliyasu

Kasa da sa'o'i 24 bayan mutuwar dan majalisar wakilai, Ja'afaru Iliyasu, wani mamba a majalisar daga jihar Kwara ya kara rasu wa.

Gidan talabijin din Channels ya bada sanarwar mutuwar dan majalisar jihar Kwara, Salihu Danladi, sanarwar na zuwa ne bayan mutuwar Ahmed Rufai a ranar Talata, 3 ga watan Disamba.

A wata takarda da mataimakon dan majalisar na musamman ya fitar, ya bayyana rasuwar dan majalisar mai wakiltar Patigi a majalisar jihar karo na 9.

Kamar yadda aka sanar, Rufai ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Ilorin a sa'o'in farko na ranar Talata.

"Da tsananin alhini tare da mika dukkan lamurra ga Allah, muna sanar da mutuwar Hon. Ahmed Saidu Rufai. Dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Patigi a jihar."

"Wannan al'amari ne da bamu yi tsammani ba kuma munyi matukar girgiza da hakan. Ubangiji bai bamu damar hana faruwar hakan ba," Danladi ya sanar.

DUBA WANNAN: Buhari ya bayar da umarnin a sake gaggauta daukan 'yan sanda 400,000

Ya kara da bayyana cewa, za a yi jana'izar Rufai kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a garin Patigi. Danladi ya yi wa mamacin addu'a tare da fatan samun rahamar Ubangiji. Ya kara da mika ta'azziya ga iyalan mamacin tare da musu fatan juriyar wannan babban rashin.

"A yayin da muke kokarin jurewa wannan lamarin, muna fatan Allah ya ji kanshi da rahama. Ya yafe mishi duk kura-kurensa, tare da ba iyalansa juriya. Muna mika ta'azziya ga majalisar jihar, masarautar Patigi, abokai da al'ummar jihar Kwara," in ji shi.

Idan zamu tuna, jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda Jafaru Iliyasu, dan majalisa mai wakiltar Magama/Rijau a tarayya ya riga mu gidan gaskiya.

An gano cewa, Iliyasu ya rasu ne a yayin baccinshi bayan da ya dawo daga Legas a daren Lahadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel