Kotun kasar Afrika ta kudu ta yankewa dan sandan shekaru 32 a gidan yari kan kisan dan Najeriya

Kotun kasar Afrika ta kudu ta yankewa dan sandan shekaru 32 a gidan yari kan kisan dan Najeriya

Wata kotun kasar Afrika ta kudu ta yankewa wani dan sandan kasar hukuncin daurin gidan kurkuku na shekaru 32 kan kisan wani dan Najeriya, Mista Ebuka Okoli.

Kotun dake unguwar Durban, Kwazulu Natal Province ta yi shari'ar ne ranar Litinin, 2 ga Disamba, 2019.

Shugaban kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta kudu, Mista Ben Okoli, ya bayyanawa manema labarai cewa: "Kotun ta yanke hukuncin shekaru 25 kan kisan kai, shekaru 2 kan fashi da makami, sannan wani shekaru uku kuma."

Kotun kasar Afrika ta kudu ta yankewa dan sandan shekaru 32 a gidan yari kan kisan dan Najeriya
Kotun kasar Afrika ta kudu ta yankewa dan sandan shekaru 32 a gidan yari kan kisan dan Najeriya
Source: Facebook

Za ku tuna cewa a kwanakin baya, an kashe yan Najeriya da dama a kasar Afrika ta kudu tare da kona musu shaguna da muhallansu.

Hakan ya tilasta shugaba Buhari zuwa kasar domin gargadi ga gwamantin jihar kan cin zarafin yan Najeriya da akeyi.

Hakazalika, Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya tsoma baki a kan rikicin kai wa bakin haure dake zaune a kasar Afrika ta kudu hari.

A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar 'yancin Inkatha, Mangosuthu Buthelezi, ya hsawarci kasashen da ake kai wa jama'arsu hari da su shigar da korafi a hukumar hadin kan kasashen Afrika (AU) tare da daukan wasu matakan idan hakan bai kawo karshen lamarin ba.

Obasanjo ya yi Alla-wadai da duk wata kasar Afrika da ta kasa magance kai wa 'yan Afrika hari a cikin kasar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel