Saraki ya yi martani bayan kotu ta bayar da umurin kwace wasu kadarorinsa

Saraki ya yi martani bayan kotu ta bayar da umurin kwace wasu kadarorinsa

Wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, jihar Legas ta bada umarnin karbar gidaje biyu na tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da ke jihar Kwara.

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tunkari kotun da ta samu shugabancin Jastis Ridwan Aikawa, da bukatar kwace wasu kadarorin Saraki da suka kai darajar Naira biliyan daya, a kan zargin da ake ya same su ne ta hanyar da bata dace ba.

EFCC ta sanar da kotun cewa “Ta zakulo wasu damfara a baitul malin gwamnatin jihar Kwara a tsakanin 2003 zuwa 2011”, lokacin da Saraki yake gwamnan jihar.

Saboda wannan bukatar, kotun ta bukaci a karba kadarorin Saraki da suka hada da gidaje biyu wadanda suke a fuloti mai lamba 10 da 11 titin Abdulkadir da ke GRA Ilorin, jihar Kwara.

DUBA WANNAN: Zamfara: APC ta yi wa Matawalle jinjina kan soke dokar biyan tsaffin shugabanni fanshon makuden kudade

Wani jami’in hukumar EFCC din, Olamide Sadiq, ya ce an mika wannan bukatar ne gaban kotun bayan binciken da hukumar yaki da rashawan ta EFCC ta yi. Kuma “rahoton kwamitin da gwamnatin jihar Kwara ta nada na bincikar siyar da gidaje a yayin mulkin Saraki tsakanin 2003 da 2011.” ya nuna akwai almundahana.

Ya ce, hukumar yaki da rashawar ta samu bayanin sirri na damfara da almnudahanar da ta faru da asusun kudin jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011.

Sadiq ya ce, “A yayin binciken, an gano cewa akwai wasu almundahana da ke boye da aka bankado”.

Amma kuma, Saraki ya jaddada cewa, wannan bukatar da aka mika wa kotun a jihar Legas ta take umarnin babbar kotun tarayya da ke Abuja. Umarni Jastis Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayyar shine "an hana wadanda suka gurfanar da shi, abokansu ko wata cibiya makamanciyar ta da ta kwace wata kadara ta wanda ake karar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel