PDP ta amince da nadin Sanata Nazif a matsayin mataimakin shugabanta na kasa

PDP ta amince da nadin Sanata Nazif a matsayin mataimakin shugabanta na kasa

- An nada tsohon dan majalisa a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa

- Kwamitin aiyukan jam’iyyar PDP ne ya amince da nada Suleiman Nazif a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar

- Nazif ya taba zama dan majalisar wakilan tarayya sau daya kuma sanatan a Najeriya sau biyu

Babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP a ranar Litinin 2 ga watan Disamba ta amince da nada Suleiman Nazif (Wakilin Arewa) a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa.

Kwamitin aiyuka na jam’iyyar PDP ne ya aminta da hakan karkashin sashi na 47, sakin layi na 6 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Nazif tsohon dan majalisar wakilai ne kuma ya yi sanata sau biyu a majalisar dattawan Najeriya. Ya shugabanci kwamitin majalisar dattawan na kan aiyuka.

DUBA WANNAN: Abinda yasa ba zamu amince da hukunci kisa ga masu satar kudin kasa ba - Majalisa Dattawa

Ya kuma yi shugaban kwamitin majalisar dattawa na hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

Nazif ya samu digirinsa na farko a jam’iar Ahmadu Bello da ke Zaria. Ya samu digirinsa na biyu daga jami’ar da ke Zaria. Nazif ya samu karramawa tare da kyautukan jinjinawa a gida Najeriya da kasashen ketare. Babban dan siyasa ne kuma jigo a jam’iyyar PDP.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito yadda shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus yace kasar nan na fuskantar tabarbarewar lamurran zabe tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulkin kasar nan a 2015.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana yadda tabarbarewar zaben ya zamo zagon kasa da kalubale ga damokaradiyyar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel