Mayakan IPOB sun kashe mataimakin kwamishinan Yansanda, da kwamandan SARS, sun banka ma motarsu wuta a jahar Anambra

Mayakan IPOB sun kashe mataimakin kwamishinan Yansanda, da kwamandan SARS, sun banka ma motarsu wuta a jahar Anambra

Tsagerun mayakan haramtacciyar kungiyar rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB sun kaddamar da wani hari a kan ayarin jami’an Yansandan Najeriya, inda suka kashe Yansanda biyu tare da banka ma motar Yansandan wuta a jahar Anambra.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin, 2 ga watan Disamba a unguwar Orafite na karamar hukumar Ekwusigo na jahar Anambra.

KU KARANTA: Mawakiyar Najeriya DJ-Cuppy za ta yi wasan kalankuwa a kasar Saudiyya

Kaakakin Yansandan jahar Anambra, Haruna Mohammed ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace: “Da misalin karfe 11:30 na safe aka kai ma Yansanda karar wani mutumi dan kungiyar IPOB ma suna Barrista Ifeanyi Ejiofor mazaunin unguwr Orafite a kan satar mutane da kuma cin zarafin jama’a.

“Bayan samun wannan rahoto sai ofishin Yansanda ta aika ma Ejiofor ya kawo kansa zuwa ofishin, amma ya ki, a dalilin haka Yansanda a karkashin babban jami’in Yansandan yankin Oliver Abbey suka bi sawunsa domin kama shi.

“Amma isarsu gidan mai laifin keda wuya, sai mayakan kungiyar IPOB suka diran ma Yansanda, tare da bude musu wuta, a sakamakon haka Yansanda biyu suka rasa rayuwarsu, sa’annan suka banka ma motar Yansandan wuta.” Inji shi.

Haruna yace baya ga yansandan da suka mutu, akwai wadanda suka samu munana rauni da dama, inda yace tuni an garzaya dasu asibiti domin samun kulawar da ya kamata. Amma rahotanni sun bayyana sunayen wadanda aka kashe da mataimakin kwamishina Oliver Abbey da kwamandan SARS Patrick Agabzue.

Daga karshe kaakakin ya kara da cewa: “Rundunar ta aika da karin jami’anta dake gudanar da sintiri a yankin tare da hadin gwiwar Sojoji da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro a yankin, tare da kokarin kama duk masu hannu cikin harin. Zuwa yanzu mun kama wasu mutane.”

Shi ma kwamishinan Yansandan jahar Anambra, John Abang ya kai ziyarar gani da ido zuwa inda lamarin ya auku, inda ya yi alkawarin zakulo duk wadanda suke da hannu cikin wannan ta’adi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel