Ina dan shekara 9 da haihuwa na zama maraya, inji Buhari

Ina dan shekara 9 da haihuwa na zama maraya, inji Buhari

- Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce ya zama maraya ne tun yana da shekaru tara a duniya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shekaru 9 da ya yi a makarantar kwana da shiga aikin soja ne ya canja rayuwarsa baki daya

- A cewar shugaban kasar, ya kamata 'yan Najeriya suyi na'am da koyan sabbin abubuwa a rayuwarsa yayin da gwamnati za ta cigaba da tallafa musu

A ranar Litinin 2 ga watan Disamba ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayar da labarin rayuwarsa yana kankanin yaro da kuma lokacin da ya ke makaranta.

Sanarwar da hadimin shugaban kasar kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu ya fitar ta ce shugaban kasar ya zama maraya tun yana karamin yaro.

Shugaban kasar ya ce shekaru tara da ya yi a makarantar kwana da shiga aikin soja ta sauya rayuwarsa baki daya.

Ya kuma ce Najeriya ilimi ne zai samarwa Najeriya cigaba na rayuwa, siyasa da tattalin arziki.

DUBA WANNAN: 2023: Akwai yiwuwar dan arewa ne zai karba mulki daga hannun Buhari, inji Babatope

Da ya ke jawabi yayin bikin cika shekaru 50 da kafa makarantar Community Secondary School, Daura inda aka karrama shi, Shugaban kasar ya yi kira ga 'yan Najeriya su rungumi ilimi a matsayin hanyar rayuwa kana gwamnati za ta yi iya kokarinta don ganin al'umma sun samu ilimin.

Shugaba Buhari ya ce, "Na shafe shekaru 9 a makarantar kwana inda malaman suka bamu cikakken kulawa da kauna. Sun dauke mu kamar 'ya'yansu da suka haifa. Suna yaba maka idan kayi abu na gari kuma za su zane ka idan kayi ba dai-dai ba."

Ya kuma yaba wa mahukunta makarantar da yanzu aka canja wa suna zuwa Pilot Secindary School, Daura kan kokarin da suka yi na tabbatar da ingancin ayyukansu yayin da kuma ya yi kira da tsaffin daliban makarantar su cigaba da ayyukan alherin da suke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel