Babu ranar bude iyakokin kasa yanzu tukuna – inji Shugaba Buhari

Babu ranar bude iyakokin kasa yanzu tukuna – inji Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya fito da kansa ya yi magana a game da rufe iyakokin kasa da aka yi. Shugaban ya nuna cewa kawo yanzu, babu ranar da za a bude iyakokin kasar.

Mai girma Muhammadu Buhari ya yi jawabi ne lokacin da ya gana da kungiyar Dattawan jihar Katsina a Mahaifarsa ta Daura. An yi wannan zama ne a Ranar Litinin, 2 ga Watan Dimsaba 2019.

Shugaban kasar ya fadawa kungiyar cewa bai sa wani takamaimen rana da za a bude iyakoki ba. Mai magana da yawun bakin shugaban kasar, Garba Shehu, ya fitar da wannan jawabi jiya.

Malam Garba Shehu ya bayyana cewa rufe iyakokin kasar na watanni biyu ya yi wa Najeriya amfani wajen yaki da masu fasa-kauri, musamman masu shigo da shinkafa ta barauniyar hanya.

Buhari ya ke cewa matakin da aka dauka ya taimaka wajen bunkasa sha’anin noma a Najeriya. Haka zalika wannan ya hutar da gwamnati wajen kashe kudi domin shigo da kaya cikin gida.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta yi magana game da dalilin rufe iyakoki

A lokutan baya, Najeriya ta kan batar da makudan kudi domin shigo da shinkafa da sauran kayan abincin da za ta iya nomawa da kanta. Wannan ya sa aka adana biliyoyin daloli a shekarun nan.

A jawabin shugaban kasar, ya kuma yabawa abin da kasar Jamhuriyyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya ta yi na taimakawa Najeriya wajen yakar fasa-kauri gadan-gadan inji Garba Shehu.

Muhammadu Buhari ya jinjinawa matakin da shugaba Muhammadou Youssoufou na Nijar ya dauka na korar wasu Jami’an kasar daga aiki tare da hana jibgewa Najeriya kayan fasa-kauri.

Wani tasirin rufe iyakar inji Buhari shi ne yanzu man da Najeriya ta ke sha a duk rana ta Allah ya ragu da fiye da 30%. Wannan ya nuna cewa a baya wasu kan sulale da man Najeriya zuwa ketare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel