Gagara gasa: Lionel Messi ya doke Ronaldo wajen lashe gwarzon kwallon kafa na 6

Gagara gasa: Lionel Messi ya doke Ronaldo wajen lashe gwarzon kwallon kafa na 6

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi ya sake lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na shekarar 2019, da wannan Messi ya kafa tarihi sakamakon karo na shida kenan yana lashewa.

A daren Litinin, 2 ga watan Disamba ne aka sanar da Messi a matsayin wanda ya lashe kyautar a wani biki daya gudana a birnin Paris na kasar Faransa inda Messi ya doke Christiano Ronaldo da dan wasan Liverpool Van Dijk.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta dauki nauyin biyan kudin WAEC da NECO ga dalibai 5000 a Adamawa

Babu wanda ya taba lashe kyautar har sau 6 a duniya sai Messi, yayin da Ronaldo ke biye da shi da guda 5, rabon Messi da lashe wannan kyauta tun shekarar 2015. Ya fara lashe kyautar ne a shekarar 2009, 2010, 2011, 2012 da 2015.

Messi ya lashe kyautar ne sakamakon a kakar wasan kwallon kafa na 2018-2019 ya zura kwallaye 51 a cikin wasanni 50, sa’annan ya bayar da kwallaye 19 an ci.

Sai dai wasu masana kwallon kafa sun yi korafin yadda Messi ya samu wannan lambar yabo duk da rashin nasarorin daya samu a wasu manyan wasanni da suka hada da rashin nasara da suka yi a hannun Liverpool a wasan gab da na karshe a gasar zakarun nahiyar turai.

Haka nan kungiyarsa Barcelona ta sha kashi a hannun Valencia a wasan karshe na gasar Copa Del rey, bugu da kari kasar Ajantina da Messi yake buga ma kwallo ta sha kashi a hannun kasar Brazil a wasan gab dana karshe na Cope America.

A bangare guda kuma, yar wasan kwallon kafa ta Amurka, kuma yar kungiyar Manchester United, Megan Rapinoe ce ta lashe kambun kwallon kafa na mata, yayin da Golan Liverpool Allison Baker ya zamto golan duniya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel