Karya ne, ba haka maganar yake ba - Maryam Uwais ta musanta dalilin da ya sa ba'a biya albashi N-Power ba

Karya ne, ba haka maganar yake ba - Maryam Uwais ta musanta dalilin da ya sa ba'a biya albashi N-Power ba

Mai baiwa shugaban Muhammadu Buhari kan shirin walwala da jin dadin al'umma, Maryam Uwais, ta musanya ikirarin ministar tallafi, manajin annoba da jin dadin al'umma, Sadiya Farouq, kan jinkirin biyan albashin ma'aikatan N-Power.

Uwais ta ce sabanin abinda ministar ta fada, sun shirya yadda za'a yi da wadanda wa'adinsu ta kare kawai aiwatarwa ake jira amma ita take jinkiri.

Mun kawo muku rahoton cewa Hajiya Sadiya Farouq ta bayyana cewa dalilin da yasa ba'a biya albashin ba shine har yanzu ba'a san yadda za'a yi da wadanda ya kamata a sallama ba duk da cewa wa'adinsu ya kare.

DUBA NAN: Dan sanda ya bindige mai mota kan karamin mujadalan da suka samu

Amma a hirar wayar tarho da Maryam Uwais tayi da Premiuim Times ranar Litinin, Uwais tace ba haka bane, an shirya yadda za'a yi da wadanda wa'adinsu ya kare tun kafin a mayar ta ofishin karkashin sabuwar ma'aikatar da Buhari ya nada Sadiya Farouq.

Ta ce gabanin mayar da ofishin karkarshinta, ita, mataimakin shugaban kasa da ministar kudi sun tattauna kan yadda za'a baiwa matasan bashin kudin jari idan aka sallamesu.

Tace: "A kan yadda za muyi da matasan N-Power, sun rubutawa gwamnoni wasiku domin ganin yiwuwan daukan wasu aiki. Mun tattauna da ma'aikatun gwamnati da dama kan hakan. Har mun tattauna da kamfanin IBM kan yadda za'a horar da su a yanar gizo."

"Mun gana da ministar Ilimi a gaban mataimakin shugaban kasa kuma mun bukaci wasu kudaden da za'a basu idan aka sallamesu."

"Bayan wannan ganawar ne aka mayar da ofishinmu karkashin sabuwar ma'aikatar. Sai na bayyana mata cewa akwai bukatar tattaunawa da ma'aikatar kudi kuma ta amince."

"Amma har yanzu shiru. Bata amsa min ba har yanzu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel