Yanzu-yanzu: Dan sanda ya bindige direban mota kan karamin mujadalan da suka samu (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Dan sanda ya bindige direban mota kan karamin mujadalan da suka samu (Bidiyo)

Labarin da muke kawo da duminsa na nuna cewa wani jami'in dan sandan Najeriya ya bindige direban babbar motar kan titi da yamman nan a jihar Ondo. TVC ta ruwaito.

Dan jaridar, Ayodeji Moradeyo ya tattaro cewa direban mai suna Ado na dauke da motoci ne inda ya nufi Abuja daga Ondo amma suka samu karamar mujadala da sandan.

Kafin kace cas! dan sandan ya bindigesa kuma take ya mutu a cikin motar.

Wannan mumunan abu ya faru ne a karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Kalli bidiyon:

Wannan ba shi bane karo na farko da jami'an yan sanda suke kashe direbobin mota kan sabanin da suka samu ba.

Irin haka ya faru a ranar Juma'a, 9 ga watan Agusta, 2019 a kan titin Kaduna zuwa Abuja inda wani jami'in dan sanda ya bindige direban mota kan cin hanci N200 da ya hanashi.

Hakan ya sa direbobin manyan motoci suka tare hanyar gaba suka hana motoci wucewa har tsawon lokaci kafin aka kwantar da kuran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel