Har ila yau: Kotu ta sake bayar da umarnin kwace wasu kadarorin Saraki da ke arewa

Har ila yau: Kotu ta sake bayar da umarnin kwace wasu kadarorin Saraki da ke arewa

Wata kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a jihar Legas ta bayar umarnin kwace karin wasu kadarorin tsohon shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki.

Alkalin kotun, Jastis Rilwan Aikawa, shine ya zartar da wannan hukunci a ranar Litinin.

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ce ta gurfanar da Saraki a gaban kotun.

Umarnin kotun ya shafi wasu gidaje ne guda biyu; mai lamba 10 da 11, da ke kan titin Abdulkadir a unguwar GRA da ke garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Ko a kwanakin baya bayan nan saida wata kotun tarayya da ke Legas ta bayar da umarnin kwace wasu manyan gidaje mallakar Saraki da ke yankin Ikoyi da ke jihar.

Saraki ya sha musanta tuhumarsa da tafka badakala da hukumar EFCC ke yi tare da bayyana cewa ya mallaki dukkan kadarorinsa ne daga kudin da yake juya wa, ba kudin gwamnati ba.

Tsohon shugaban majalisar ya sha bayyana cewa bai saci ko sisi ba daga aljihun gwamnati a lokacin da yake gwamna a jihar Kwara da kuma lokacin da ya kasance shugaban majalisar dattijai.

A cewarsa, gwamnatin tarayya na yin amfani da hukumar EFCC ne domin kawai muzguna masa saboda wasu dalilai na siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel