Tashin hankali: An kama wani mutumi da ya yiwa akuyoyi guda biyu fyade har suka mutu

Tashin hankali: An kama wani mutumi da ya yiwa akuyoyi guda biyu fyade har suka mutu

- Wani abin kunya da wani mutumi yayi ya gama yaduwa a shafukan sada zumunta, inda mutane da yawa suke ta Allah wadai da wannan abu da yayi

- An dai kama mutumin da laifin yiwa wasu akuyoyi guda biyu fyade, inda har ta kai ga duka sun mutu saboda wahala

- Yanzu haka dai mutumin ya shiga hannun 'yan sanda inda har yayi kwana daya a hannunsu, amma an bayar da belin shi akan kudi masu tarin yawa bayam ya nemi ayi masa sassauci

Wani mutumi da aka bayyana sunan shi da Mbiti Munyao dake garin Kangundo dake yankin Machakos dake kasar Kenya, an kama shi da laifin yiwa akuyoyi guda biyu fyade inda har suka mutu saboda bala'i.

A cewar shugabar hukumar 'yan sanda ta yankin Chief Mary Mulwa, an gano Munyao yana jawo akuyoyin guda biyu daga cikin daji wajen da aka daure su ranar Asabar 13 ga watan Janairun wannan shekarar. Akuyoyin guda biyu duka sun mutu jim kadan bayan Munyao ya gama yi musu fyade.

An kama mai laifin inda ya kwana a ofishin 'yan sanda kafin daga baya a bayar da belin shi akan kudi naira sama da naira dubu dari uku, bayan ya amsa laifin shi ya kuma roki ayi masa sassauci.

KU KARANTA: Mai Tabargaza: Jarumar fim da ta sha tabar wiwi da shafin Bible ta ce a shirye take ta yayyaga Al-Qur'ani idan aka bata

Ana tuhumar mai mutumin da laifin kashe akuyoyin ta hanyar da bai kamata ba.

Hotunan akuyoyin dana mutumin a lokacin da yake a ofishin 'yan sanda na kasar ya gama yaduwa a shafukan sada zumunta na kasar Kenya, inda mutane da yawa suke ta Allah wadai da wannan abu da mutumin yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel