Kasar Benin ba ta yi hankali ba duk da rufe iyakoki – Inji Ministan Najeriya

Kasar Benin ba ta yi hankali ba duk da rufe iyakoki – Inji Ministan Najeriya

Mun samu labari cewa Gwamnatin Najeriya ta fito ta yi magana game da rufe iyakokinta na kasa da ta yi. Gwamnatin ta kare wannan mataki ne ta bakin Ministan yada labarai da al’adu.

Najeriya ta ce kasar Benin ba ta nuna da-na-saninta bayan ta jawo an rufe iyakokin ba. Gwamnatin kasar ta yi wannan jawabi ne ta bakin Alhaji Lai Mohammed a cikin karshen mako.

Lai Mohammed ya zargi makwabtan Najeriya da laifin shigo da kayan da aka haramta, sannan su jibge a Najeriya, Lai Mohammed ya ce wannan aiki ya sa aka dole Najeriya ta rufe iyakokinta.

Kayan da ake cigaba da karbewa daga Benin duk da rufe iyakoki, ya nuna cewa kasar ba ta tuba ba. Shigo da haramtattun kaya ya sabawa dokoki da yarjejeniyar ECOWAS na kasashen Nahiyar.

Lai ya ce abin da su ke gani ya tabbatar da cewa Benin ba za ta iya bin dokokin kasuwancin da Najeriya ta gindaya ba. Ana yawan shiga da fita da kaya daga Benin da Nijar zuwa Najeriya.

KU KARANTA: Buhari ya yi daidai da ya rufe iyakar Najeriya - Jigon adawa

“Abin da-na-sanin shi ne, alamun da mu ke gani a ‘yan makonnin ba su da kyau ganin irin kayan da mu ke karbewa daga makwabatunmu ya nuna cewa ba su da shirin bin dokokin Najeriya.”

Ministan yada labaran ya tabbatar da cewa Najeriya za ta cigaba da rufe iyakokinta domin taimakawa kayan gida. Za a cigaba da barin iyakokin a rufe na tsawon lokacin da ya dace.

Mai girma Ministan ya ce Najeriya ba za ta cigaba da taimakawa kasashen Nahiyar, yayin da tattalin arzikinta da sha’anin tsaro ya ke fuskantar barazana a dalilin barnar makwabta ba.

Gwamnatin ta shugaban kasa Buhari ta jaddada matsalolin da ta ke samu daga kasashen Benin da Nijar. Lai ya kare matakin hana kai fetur bakin iyaka da cewa ana haurawa da su ketare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel