Yanzu-yanzu: Buhari ya kaddamar da fara ginin jami'ar Sufuri a garin Daura (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Buhari ya kaddamar da fara ginin jami'ar Sufuri a garin Daura (Bidiyo)

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara ginin sabuwar jami'ar koyar da ilimin Sufuri a mahaifarsa dake Daura, jihar Katsina.

A yanki filin gina jami'ar ne a karamar hukumar Sandamu ta jihar Katsina.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan inda ayace:

"An kafa tarihi! Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin gina sabuwar Jami'ar Sufuri a Daura."

Kamfanin gine-ginen kasar Sin wato China Civil and Construction Company (CCECC), ce za ta gina jami'ar irinta na farko (a Najeriya)."

Source: Legit

Tags:
Online view pixel