Bayan samun nasara a zabe: Yahaya Bello ya sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa a Kogi

Bayan samun nasara a zabe: Yahaya Bello ya sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa a Kogi

A ranar Litinin ne Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sauke duk wasu nade-nade da yayi a zangon mulkinsa na farko.

Ya umarci hadiman da ya sauke da su mika duk wasu kadarorin gwamnati da ke tare dasu zuwa ga shugabannin wuraren da suke aiki.

A takardar da sakataren gwamnatin jihar, Dr. Ayoade Folashade, yasa hannu a kai, gwamna Bello ya ce duk wadanda aka nada a karkashin ofishin mataimakinsa, uwargidansa, da kuma uwargidan mataimakinsa, lamarin bai shafesu ba.

A wata takardar da sakataren yada labaran gwamnan, Onogwu Mohammed ya fitar, ya kara haske a kan wadanda abun ya shafa.

"Wadannan jama'ar basu cikin wadanda umarnin ya shafa: Dukkan kwamishinoni, darakta janar na gidan gwamnati, hadiman gwamna na kai tsaye, hadiman mataimakin gwamna na kai tsaye, hadiman shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, hadiman uwargidan gwamnan da kuma hadiman uwargidan mataimakin gwamnan," kamar yadda yake a cikin takardar.

Takardar ta kara da cewa, shugaban ma'aikata, shugaban fannin kididdiga na jihar da kananan hukumomi duk umarnin bai shafesu ba.

Ga wadanda abin ya shafa, ana sa ran zasu kammala shirin ajiye aikin ne a ranar Talata, 3 ga watan Disamba 2019.

"Zasu mika kwafin takardun ajiye aikinsu ne ga sakataren gwamnatin jihar Kogi.

" Gwamnati na mika godiyarta ga wadanda abun ya shafa sakamakon rawar da suka taka da kuma gudummawar da suka bada don habaka jihar Kogi," in ji takardar.

Idan zamu tuna, kwanan nan gwamnan jihar Kogi ya lashe zaben kujerar gwamnan a karo na biyu. An yi zaben ne a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel