Yanzu-yanzu: An zabi sabon Kakin Majalisar dokokin jihar Taraba

Yanzu-yanzu: An zabi sabon Kakin Majalisar dokokin jihar Taraba

Da safiyar Litinin, 2 ga Disamba, mambobin majalisar dokokin jihar Taraba suka zabi, Joseph Albasu Kunini. matsayin sabon kakakin majalisar tare da Alh Hamman Adama Abdulahi matsayin mataimakinsa.

Hakan ya biyo bayan murabus da tsohon Kakakin majalisa, Abel Peter da mataimakinsa, Maijankai Charles sukayi ranar Lahadi.

Yan majalisar sun nada tsohon mataimakin kakakin majalisar, Alh Muhammad Gwampo, matsayin kakakin yan mintuna kadan domin jagorantan zaben sabon kakaki.

Sakamakon zaben ya nuna cewa dukkan yan majalisu 16 da suka halarci zaman sun zabi Joseph Albisu.

Bayan rantsar da shi, Kakakin ya jagoranci zaben mataimakin kakaki inda aka zabi Alh Bashir Muhammad, ba tare da wani abokin hamayya ba.

A jawabinsa na farko, Kunini ya bayyana godiyarsa ga abokan aikinsa da suka bashi wannan damar kuma ya yi alkawarin aikata gaskiya da adalci.

Sabon kakakin ya yi alkawarin tabbatar da cewa ya hada kan yan majalisar domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Albasu Kunini yana wakiltar mazabar Lau ne kuma tsohon dan majalisa ne.

Bugu da kari, majalisar ta zabi Mista Douglas Isaiah a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel