Yanzu-yanzu: Ganduje ya sake gabatar da kudirin kafa sabbin masarautu 4 ga majalisa

Yanzu-yanzu: Ganduje ya sake gabatar da kudirin kafa sabbin masarautu 4 ga majalisa

Bayan ya makonni da wata babbar kotun jihar Kano ta soke sabbin masarautu hudu a jihar Kano, gwamnatin jihar ta gabatar da sabon kudiri ga majalisar dokokin jihar domin sake kafa wadannan masarautu.

Jawabin da kwamishanan yada labaran jihar Kano, Mohammaed Garba ya saki kuma ya rattafawa hannu ya bayyana cewa majalisar zantarwan jihar ta yanke shawaran sake gabatar da kudirin ne a daren Lahadi, 1 ga watan Disamba, 2019.

Sabbin masarautun da aka gabatar sine Rano, Gaya, Bichi da Karaye.

Mohammed Garba ya bayyana cewa majalisar zantarwan ta tattauna lamarin kafa sabbin masarautun da aka kwashe shekaru goma ana bukata domin samar da cigaba da alfanu ga al'ummarsu.

Ya ce an samar da wasu daga cikin sabbin masarautun kafin Kano amma an gaza dawo da su.

Za ku tuna cewa a ranar 21 ga watan Nuwamba, Wata babbar kotu a jihar Kano, karkashin jagorancin Jastis Usman Na'Abba ta soke karin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta kirkiro.

A yayin yanke hukunci a ranar Alhamis, kotun ta ce, majalisar jihar Kano ta yi karantsaye ga tanadin sashi na 101 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ya ba 'yan majalisar damar zartar da doka.

DUBA WANNAN: An zabi sabon Kakin Majalisar dokokin jihar Taraba

Tun bayan fitowar maganar kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano, Mutane da yawa sun ta tunanin Gwamna Ganduje na yakar Sarki Sanusi ne ta ruwan sanyi bayan banbancin da suka samu a zaben 2019.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel