Goodluck Jonathan ya soki shugabannin da ke kashe rai saboda kujerar mulki

Goodluck Jonathan ya soki shugabannin da ke kashe rai saboda kujerar mulki

Jaridar The Cable ta rahoto tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya na rokon shugabanni da ‘yan siyasa da su daina kashe rai don kurum su ka cigaba da zama a kan karaga.

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan kira ne bayan karrama sa da aka yi da Digirin Dakta a fannin kimiyya jami’ar Igbinedion da ke Garin Okada a jihar Edo, a cikin karshen makon jiya.

An yi wannan taro ne a Ranar Asabar, 30 ga Watan Disamban 2019. Jonathan ya yi amfani da wannan dama wajen jan kunnen masu mulki da ke kashe mutane saboda su zauna a kan kujera.

Dr. Goodluck Jonathan ya yi Allah-wadai da wannan mummunar yunwa ta wasu ‘yan siyasar kasar. Jonathan ya ce ‘yan siyasar Afrika sun kawo sabon salon juyin-mulki a tsarin farar hula.

Duk da Sojoji sun daina mulki, Jonathan ya ce ‘yan siyasa sun shigo da salon hambarar da gwamnati ko juyin mulki a cikin tsarin damukaradiyya na farar hula da ake aiki da shi a kasar.

KU KARANTA: Ana zargin Jonathan da shiryawa PDP makarkashiya a Bayelsa

Ganin abin da ya faru kwanan nan, Goodluck Jonathan ya ce: “Bari in roki Abokai na ‘yan siyasa, su daina kashe jama’a, su na rusa dukiyoyinsu, domin kurum su na neman mukami a gwamnati.

“Abin da ya faru a zaben baya na gwamnoni a jiha ta ta Bayelsa, da kuma Kogi, musamman a jihar Kogi, inda aka kona wata Mata da ranta a cikin gida ta, bai kamata ya faru a cikin al’umma ba.”

Tsohon shugaban kasar ya nuna cewa kashe ‘yar siyasar da aka yi ba daidai bane, kuma ya nuna matsalar tsarin siyasar mu. Jonathan ya ce hakan bai dace da al’umma da ke tafiya daidai ba.

“Jiyan nan (Juma’a) mu ke labarin siyasa da sauran Takwarori na, tsofaffin shugabannin kasashe da mataimakanmu. Yadda ake siyasa a Afrika ba zai kai Nahiyar ga ci ba.” Inji Dr. Jonathan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel