Ba Gwamnoni kurum Matar Shugaban kasa ta yi wa huduba a taron NSCIA ba – Inji NGF

Ba Gwamnoni kurum Matar Shugaban kasa ta yi wa huduba a taron NSCIA ba – Inji NGF

A jiya Ranar Lahadi, 1 ga Watan Disamban 2019, Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya a karkashin kungiyar su ta NGF, su ka maida martani kan wasu kalamai na Matar shugaban kasar Najeriya.

Gwamnonin kasar sun caccaki rahotannin da aka fitar a kan Uwargidar ta na gargadin gwamnoni da cewa abubuwa sun kama hanyar tabarbarewa a halin yanzu a kasar nan.

Shugaban harkar yada labarai da hulda da manema labarai na kungiyar NGF, Alhaji Abdulrazaque Bello Barkindo ya fitar da jawabi inda yace kalaman Matar shugaban kasar sun zo a daidai.

Jaridar Vanguard ta rahoto raddin gwamnonin ya na cewa: “Sukar da Aisha Buhari ta yi a babban masallacin musulmai na Abuja wajen taron kungiyar NSCIA ya zo a mafi kyawun lokaci.”

Akwai bukatar Matar shugaban kasa da kanta, ta fadawa Malamai cewa abubuwa sun kama layin tabarbarewa, wannan ba gwamnoni kurum ya taba ba, kamar yadda ake nema a nuna.”

KU KARANTA: Yadda Buhari zai kashe Najeriya - Atiku Abubakar

Kungiyar gwamnonin ta ce daukacin ‘yan siyasar kasar nan Aisha Buhari ta daurawa laifin halin da aka samu kasar. NGF ta ce wasu ne ke kokarin nuna cewa da gwamnoni kurum ta ke magana.

“Abin takaici, gaggawan bata gwamnonin jihohi ya sa aka cika gaban jaridu da wannan labari, aka wargaza ainihin sakon da Uwargidar shugaban kasar ta isar.” Inji Abdulrazaque Barkindo.

NGF ta cigaba da kare Buhari ta na cewa: “Hajiya Buhari ta yi wa kowane mai mulki huduba ne da su ji tsoron Allah a duk inda su ka samu kansu, domin kuwa za su amsa tambayoyi a gaba.”

Kungiyar ta kara da cewa: “Yunkurin nuna cewa da gwamnoni kurum Uwargidar kasar ta ke da cewa jama’a su na fama da rashin ruwa, bai nuna cewa gwamnoni kadai za su hadu da Ubangiji.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel