Yan ta’adda sun bude ma kiristoci wuta a coci, sun kashe 14 a Botswana

Yan ta’adda sun bude ma kiristoci wuta a coci, sun kashe 14 a Botswana

Wasu gungun yan ta’addan kungiyar ta’addanci sun kaddamar da harin mai kan uwa da wabi a wani coci dake kasar Burkina Faso inda suka kashe mutane 14 nan take, yayin da wasu da dama suka samu munana rauni.

Jaridar Premium Times ta ruwaito yan bindigan sun kai wannan samame ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Disamba yayin da mabiya darikar Protestant na addinin kirista suke gudanar da bauta a cocin dake yankin hantoukoura na kasar.

KU KARANTA: Gwamna Matawalle ya fitar da daliban Zamfara 200 domin karo karatu a kasashen duniya

Shugaban kasar Botswana, Roch Kabore ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya bayyana harin a matsayin lamari mai muni wanda jahilai ne kadai ke aikata shi, sa’annan ya jajanta ma iyalan mamatan da wadanda suka samu rauni.

Wannan hari ya zo ne a daidai bayan kwanaki 60 da mutane 37 suka mutu a yayin wani hari da wasu gungun yan bindiga suka kai a wani sansanin hakar ma’adanan kasa, inda suka jikkata akalla mutane 60.

Kasar Botswana, wanda a baya ke lissafata cikin jerin kasashen Afirka da suka fi zaman lafiya ta shiga mawuyacin hali da rashin tsaro ne tun a shekarar 2015 lokacin da yan bindiga suka fara kai farmaki, tare da ayyukan yan fashi, garkuwa da mutane da sauran miyagu .

Da wannan a ranar 27 ga watan Nuwamba gwamnatin kasar Amurka ta gargadi jama’anta dasu kauce ma zuwa kasar sakamakon hauhawar matsalar tsaro a kasar, wanda hakan yasa ba zasu basu tabbacin kulawa da lafiyarsu, rayukansu ko dukiyoyinsu ba.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sanye da khakin NYSC sun bude ma wasu yan kwallon Najeriya wuta na kungiyar kwallon kafa ta Ifeanyi Ubah FC a garin Okene na jahar Kogi.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba a yayin da yan kwallon suke kan hanyarsu ta zuwa jahar Kano inda zasu kara da kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Starts a gasar zakarun Najeriya, a ranar Lahadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel