Gwamna Matawalle ya fitar da daliban Zamfara 200 domin karo karatu a kasashen duniya

Gwamna Matawalle ya fitar da daliban Zamfara 200 domin karo karatu a kasashen duniya

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya sanar da gwamnatinsa ta dauki nauyin matasa 200 yan asalin jahar Zamfara domin yin karatu a wasu jami’o’I dake kasashen duniya guda.

Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga daliban da suka samu nasarar samun wadannan duraben karatu a karkashin tsarin bada tallafin ilimi na gwamnatin jahar Zamfara, inda ya yi kira a garesu da su kasance yan kasa nagari masu kishin jaharsu a inda zasu tafi karatun.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Buhari zai gina sabuwar jami’ar rundunar Sojan sama a Bauchi

A jawabinsa, gwamnan yace daga cikin daliban akwai guda 30 da zasu yi karatu a kasar India, guda 50 a kasar Sudan, guda 50 a kasar China da kuma guda 70 a kasar Cyprus, kuma dukkaninsu zasu karanci fannonin da suka danganci kiwon lafiya da kuma kimiyya da fasaha ne.

“Burina ne na inganta fannin ilimi a jahar Zamfara, musamman abin da ya shafi harkar matasa, shi yasa ma daga cikin nade naden dana fara yi a gwamnatina akwai ofishin mai baiwa gwamna shawara a kan harkar tallafin karatu da sha’anin dalibai.

“Mun baku wannan dama ne domin fahimtar kwazonku da kuma fatan zaku yi amfani da ilimi da kwarewar da zaku samu wajen sauya rayuwar al’ummar jahar Zamfara tare da kawo cigaba a yankunanku da ma jahar gaba daya.

“Don haka zaku shiga cikin mummunan tarihi idan har kuka sake kuka yi wasa da wannan dama, kuka kasance tamkar masu yawon bude idanu a kasashen da zaku tafi karatu a maimakon ku yi karatun, don haka nake kira a gareku ku jajirce wajen yin karatu tare da daukansa da muhimmanci. Mu kuma zamu cigaba da baku duk gudunmuwar daya kamata don ganin kun samu nasara.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan ya lallashi sauran daliban da suka nemi wannan dama amma basu samu ba da cewa wannan somintabi ne, domin kuwa gwamnatinsa za ta cigaba da neman ire iren guraben karatun nan domin taimaka ma daliban jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel