El-Rufai ya yi martani ga EFCC kan zargin batan N32bn a yayin da yake ministan FCT

El-Rufai ya yi martani ga EFCC kan zargin batan N32bn a yayin da yake ministan FCT

A ranar Lahadi, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yace bai taba hana hukumar yaki da rashawa ta EFCC da ta yi aikinta ba. A maimakon hakan, ya garzaya kotu ne don wanke kanshi.

A takardar da lauyan El-Rufai, A.U Mustapha (SAN) ya fitar, ya ce gwamnan jihar Kaduna ya tunkari kotun ne a 2009 don ya wanke sunansa daga baci.

Mustapha ya ce, "EFCC ta baza a kafafen yada labarai yadda N32bn ta bace, lamarin da yasa Malam El-Rufai ya nufi kotu don bayani dalla-dalla."

Idan zamu tuna, takardar ta bayyana yadda El-Rufai lokacin da yake ministan tarayya ya siyar da wasu filaye a Abuja. Ya kuma shugabanci siyar da wasu gidajen a babban birnin tarayyar, wanda hakan ya kawo wa gwamnatin tarayyar kudi har naira biliyan 32.

DUBA WANNAN: APC ta kara kayar da PDP a zaben maye gurbi a jihar Katsina

Lauyan El-Rufai ya tunatar da cewa, tsananin siyasantarwa ce ta sa hukumar yaki da rashawa ta EFCC din ta ke shafawa mutane kashin kaji.

Babban lauyan ya ce, El-Rufai ya garzaya kotu ne don tantance abubuwa uku masu muhimmanci. kamar haka, "Kotun ta tantance mai kara, wanda a lokacin da yake ministan tarayya ko ya bi sharuddan da majalisar zartarwa ta tarayya ta gindaya na siyar da gidaje daga watan Mayu 2005 da watan Mayu 2007."

Mustapha ya kara da cewa, El-Rufai ya bukaci abubuwa guda 7 daga kotun wadanda suka hada da "takardar shaidar cewa an siyar da gidajen gwamnatin tarayyar kamar yadda majalisar zartarwa ta tarayya ta gindaya ta hannun kwamitin wucin-gadin da ta nada na siyar da gidajen".

Lauyan El-Rufai ya ce, "Muhimmin abu a nan shine, kotun ta bada duk bayanan da wanda muke karewa ya bukata kuma mun gamsu da hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel