Sahihan dalilan da suka sa aka fincike kakakin majalisar jihar Taraba

Sahihan dalilan da suka sa aka fincike kakakin majalisar jihar Taraba

An gano dalilin da yasa Diah ya samu fushin Gwamna Ishaku bayan ya shige gaba wajen nemawa majalisar damar zartarwa kai tsaye. Tuni aka binciko sahihin dalilin da yasa Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya fincike kakakin majalisar jihar, Abel Diah.

Gwamna Ishaku ya sha mamaki da ya gano yunkurin Diah wajen samar wa majalisar jihar karfin ikon yanke hukunci a jihar, amma hakan ya gagara.

Wani na sahun gaba a gwamnatin jihar ya bayyana cewa, "Gwamnan ya ji ba dadi bayan da ya gano yadda Diah ya shiga sahun gaba wajen nemawa 'yan majalisar jihar yancin mulkin ba tare da dogaro ba, yayin da suka yi taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin kwanakin nan."

DUBA WANNAN: APC ta kara kayar da PDP a zaben maye gurbi a jihar Katsina

Duk da cewa, taron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da kakakin majalisun jihohi 36 na sirri ne, an gano cewa makasudin wannan taron shine neman yancin tare da dogaro da kai na majalisun ne.

Majiyar ta ce, Gwamna Ishaku ya yanke hukuncin koyawa Diah darasi ne a kan matsayarshi a nemawa majalisar yanci tare da dogaro da kanta.

Da yawa daga cikin 'yan majalisar jihar sun bi ayarin kamfen din sauke kakakin majalisar, kuma da hakan ne suka yi amfani wajen fincike Diah daga kujerar kakakin majalisar jihar Taraba din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel