Za ka kashe Najeriya da bashi - Atiku ya caccaki Buhari

Za ka kashe Najeriya da bashi - Atiku ya caccaki Buhari

Tsohon shugaban kasan Najeriya kuma dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasan 2019, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari kan karban basussuka.

Ba tare da sassautawa shugaban kasa ba, Atiku a kaikaice ya gorantawa shugaba Buhari kan rashin kasancewarsa dan kasuwa shi yasa yake karban basussuka yadda ya dama.

Atiku ya ce babu wani dalilin da zai sa a karbi bashi domin biyan albashi yayinda ba'a sa hannun jari cikin rana goben yan Najeirya ba.

Yace: "A matsayin dan kasuwa, abu na farko da za kayi la'akari da shi ne kada ka karbi bashi muddin ba fadada kasuwancinka za kayi ba. Hakazalika, babu wani dalilin da zai sa a karbi bashi domin biyan albashi."

Atiku ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su mayar da hankali kan bangaren Ilimi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kakakin majalisar dokokin jihar Taraba ya yi murabus

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya soki Buhari kan rashin baiwa bangaren Ilimi isasshen kudi domin inganta ilimi a Najeriya.

Ya jaddada cewa rashin baiwa sashen ilimi kaso mai tsoka na nuna cewa ikirarin gwamnatin Buhari na yakan ta'addanci maganar baka ce kawai;

Atiku ya bayyana wannan ne a taron tunawa da mu'assasin jami'ar Amurka dake Yola, jihar Adamawa, mallakin Atiku Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel