2019: Sanata Dino Melaye ya yi waka a game da zaben da ya rasa

2019: Sanata Dino Melaye ya yi waka a game da zaben da ya rasa

Sanata Dino Melaye wanda ya rasa zaben majalisar dattawa a jihar Kogi a karshen makon nan, ya fito da wata sabuwar waka, daga kammala zabe.

Dino Melaye wanda ya sha kashi a hannun Sanata Smart Adeyami ya fito da wannan waka ne a yau, Ranar Lahadi 1 ga Watan Disamban 2019.

Fitaccen ‘dan majalisar ya yi wannan waka ne da yarbanci, ya na mai nuna cewa Ubangiji ba mutum ba ne, don haka ya ke sa ran nasara.

Melaye ya wallafa wannan bidiyo ne da karfe 5:20 na yamma a dandalinsa na shafin Tuwita. Watakila an dauke bidiyon ne cikin gidansa.

An ga tsohon Sanatan ya na rawa a wannan bidiyo da yanzu jama’a da-dama su ke ta magana a kai a kafafen yada labarai da sada zumunta.

KU KARANTA: Dino Melaye ya bayyana a wani shirin wasan kwaikwayo

Kawo yanzu mutane fiye da 700 sun tofa albarkacinsu game da bidiyon. Haka zalika mutane kusan 6000 sun kalli bidiyon wannan waka a Tuwita.

Sanatan ya fito ya na cewa ko da wasu mutane ko malamai sun nuna cewa mutum ya tabe, wannan bai canza abin da Ubangiji ya rubuta.

Mista Melaye ba bako bane wajen fitowa ya yi magana a shafinsa na Tuwita. Idan ba ku manta ba, ya kuma taba fitowa a shirin wasan kwaikwayo.

A baya tsohon ‘dan majalisar kasar ya yi ikirarin cewa an murde karashen zaben da ya rasa da ratar kuri’u 20, 000 wajen Smart Adeyami na APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel