Kano: Shugaban kasa Buhari ya aika ta’azziya da Iyalin Tijjani Rabiu

Kano: Shugaban kasa Buhari ya aika ta’azziya da Iyalin Tijjani Rabiu

A Ranar Lahadi, 1 ga Watan Disamba, 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nuna girgizarsa game da rasuwar babban ‘Dan kasuwan nan na jihar Kano, Attajirin Tijjani Rabiu.

Shugaban kasar ya mika gaisuwar ta’aziyyarsa ga Iyalin mamacin da daukacin al’ummar jihar Kano game da wannan rashi. Shugaban kasa Buhari ya kira wannan rashi da faduwar wata giwa.

Garba Shehu, daya daga cikin Mai magana da yawun bakin shugaban kasa Buhari, ya fitar da wannan jawabi a yau da rana. Marigayin ‘Danuwa ne wurin Attajirin da aka yi, Isyaku Rabiu.

Buhari ya bayyana mutuwar Rabiu da faduwar wani Bajimin ‘Dan kasuwa da fatauci a Arewacin Najerya. Shugaban kasar ya kuma ce, tun da aka kafa kasar nan aka san da sunan da su Rabiu.

KU KARANTA: Sanatan PDP ya komawa Allah bayan ya sha kasa a zaben 2019

Jawabin shugaban kasar ya ce: “Marigayin ya na cikin daular ‘yan kasuwar da su ka yi farin-jini tun da aka kirkiri Najeriya, wanda ya kai ga nasara ta hanyar namijin kokari da jajircewa.”

"Lokacin da ya ke raye, Rabiu ya bi tafarkin Yayansa kuma ya na cikin wadanda aka rika bugawa da su a sha’anin kasuwanci. Bayan nasara a kasuwanci, Dangin Rabiu sun yi fice wajen Malanta."

Shugaban Najeriyar ya yi kira ga Matasan kasar nan su yi koyi da irin wadannan Attajirai. A cewarsa, neman kudi da gumin halas ya fi albarka a kan neman miyagun dabarun samun dukiya.

Marigayi Isiyaka Rabiu fitaccen ‘dan kasuwa ne kuma attajiri da aka yi a Arewacin Najeriya wanda ya rasu ya na da shekaru fiye da 90. Gidansu ya yi fice a addini na Darikar Tijjaniyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel