Zaben Bayelsa: Rikici ya kaure tsakanin manyan PDP a kan binciken da Jonathan

Zaben Bayelsa: Rikici ya kaure tsakanin manyan PDP a kan binciken da Jonathan

Makonni uku da yin zaben gwamna a jihar Bayelsa, ana ta fama da sabani a cikin jam’iyyar PDP. Wannan ya na zuwa ne bayan jam’iyyar APC ta yi nasarar lallasa PDP a zaben sabon gwamnan.

Kamar yadda rahotanni su ke zuwa mana, wasu ‘Ya ‘yan PDP su na kira a hukunta tsohon shugaba, Goodluck Jonathan a dalilin zargin taimakawa jam’iyyar adawa ta APC da ya yi a zaben.

Wasu su na zargin akwai hannun Dr. Goodluck Jonathan wajen nasarar da jam’iyyar hamayya ta samu a zaben gwamnan. Wannan ne karon farko da PDP ta fadi zaben jihar a cikin shekaru 20.

The Nation ta rahoto wasu ‘Yan cikin gidan PDP sun kai ziyara zuwa Hedikwatar jam’iyyar domin tattaunawa game da wannan lamari. Jaridar ta ce yanzu haka wannan batu ya jawo sabani.

Wannan kira na binciken tsohon shugaban kasar ya yi sanadiyyar sabanin da aka samu tsakanin jami’an jam’iyyar na NWC. Wani Jagorran jam’iyyar a Bayelsa ya ce dole a hukunta masu laifi.

KU KARANTA:

Jigon ya ce: “Mu da mu ke kira a binciki abubuwan da su ka auku har su ka kai ga faduwar PDP a zaben Bayelsa, mu na yin wannan ne domin ganin an cigaba da samun tarbiya a jam’iyyar.”

Ana zargin cewa wani gwamnan Neja-Delta ya na cikin masu baza wuta domin a gudanar da bincike kan yadda tsohon shugaban ya yi wa jam’iyyarsa zagon-kasa a zaben gwamnan jiharsa.

Mu na samun labari cewa akwai wani wanda ya taba neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a cikin masu kira ga uwar-jam’iyya ta binciki zargin da ke kan wuyan jagoran jam’iyyar.

Masu yin wannan kira, su na da ra’ayin cewa babu dalilin da za a kyale wani ya gagari jam’iyya, komai girmansa. Sai dai kuma wani cikin kwamitin amintattu na BOT, ya ce ba za ta sabu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel