APC ta kara kayar da PDP a zaben maye gurbi a jihar Katsina

APC ta kara kayar da PDP a zaben maye gurbi a jihar Katsina

Jam'iyyar PDP mai adwa ta bayyana rashin gamsuwarta da sakamakon zaben mayen gurbin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewa jam'iyyar APC ce ta samu nasarar lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba.

Da take sanar da sakamakon zaben ta bakin baturenta, hukumar INEC ta bayyana cewa Ibrahim Danjuma na jam'iyyar APC ne ya samu nasarar lashe zaben maye gurbin kujerar dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Sabuwa.

Danjuma ya samu jimillar kuri'u 11,745 yayin da babban abokin hamayyarsa, Ibrahim Shafiu, dan takarar jam'iyyar PDP, ya samu jimillar kuri'u 6,160.

Sauran 'yan takarar da suka zaben sun hada Sagir Bako na jam'iyyar MPN; ya samu kuri'u 11, Idris Sabiu na jam'iyyar NLDP; ya sanu kuti'u 7, da kuma Dahiru Ahmed na jam'iyyar PDC; wanda ya samu kuri'u 15.

A cewar baturen zaben, Dakta Usman Adamu Bello na jami'ar Ahmadu Bello d ke Zaria, an tantance masu kada kuri'a 18,572, sannan an kada jimillar kuri'u 18,276 a zaben.

DUBA WANNAN: Yadda mulkin mahaifina ya mayar da ni tamkar wata 'Mujiya' - Zahra Buhari

Ya bayyana cewa an samu kuri'u sahihai 17,938, yayin da kur'u 338 suka lalace.

Da yake martani a kan sakamakon zaben, shugaban jamiyyar PDP a jihar Katsina, Salisu Majigiri, ya fada wa manema labarai an tafka magudi kala daban-daban yayin zaben, sannan kuma an saba wa dokokin zabe.

Ya kara da cewa jam'iyyarsu zata kalubalanci sakamakon zaben a kotun sauraron korafin zabe.

An gudanar da zaben ne domin maye gurbin tsohon dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Sabuwa, wanda ya mutu sakamakob hatsarin mota da ya ritsa da shi a cikin watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel