Aisha ta kare Buhari a kan kin gaisawa da Tinubu a wurin taro

Aisha ta kare Buhari a kan kin gaisawa da Tinubu a wurin taro

- Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta kare mijinta a kan kin gaisa wa da matar Bola Tinubu, Sanata Remi Tinubu

- Faifan bidiyon yadda shugaba Buhari yayin da ya tsallake Sanata Tinubu yayin gaisawa da jama'a ya jawo cece-kuce a dandalin sada zumunta

- Uwargidan shugaban kasar ta dora alhakin tsallake Sanata Tinubu da Buhari ya yi a kan ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta kare mijinta a kan kin gaisa wa da Sanata Remi Tinubu a wurin wani taro da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya halarta.

Aisha ta yi martani ne yayin da faifan bidiyon shugaban kasa Buhari ke yawo a dandalin sada zumunta domin nuna yadda ya tsallake Sanata Tinubu yayin da yake gaisa wa da mutane.

DUBA WANNAN: Yadda mulkin mahaifina ya mayar da ni tamkar 'Mujiya' - Zahra Buhari

Uwargidan shugaban kasar ta yi zargin cewa ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya dauke wa shugaba Buhari hankali zuwa kan wani namiji da ke kan layin mutanen da zasu gaisa da shi.

Da take magana a kan faifan bidiyon, Aisha ta rubuta cewa, "ba zan zargi shugaban kasa ba, @DrIsaPantami ya dauke hankalinsa zuwa kan namiji da ke kan layin. Watakila ya yi hakan ne don baya son ganin shugaban kasa ya gaisa da mace a kan idonsa. Ministan bai kamata ya yi haka ba!"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel