Mai Gida na kadai ba zai iya shawo kan matsalolin mu ba – Aisha Buhari

Mai Gida na kadai ba zai iya shawo kan matsalolin mu ba – Aisha Buhari

Mun samu labari, Matar Shugaban kasa watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta ja kunnen jama’a, inda ta ce akwai tarin matsaloli da su ka zama kalubale ga kasar nan a halin yanzu.

Mai girma Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana cewa abubuwa su na neman cin tura. Uwargidar ba ta tsaya a nan ba, ta nuna cewa sai an dafawa Mai gidanta shugaban kasa Buhari.

A cewar Buhari, shugaban kasa ba zai iya kawo karshen matsalolin da ake fuskanta shi kadai ba. Wannan ya sa ta nemi sauran ‘yan siyasa da masu rike da mukamai su bada ta su gudumuwa.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Uwargidar Buhari ta yi wannan jawabi ne jiya Asabar, 30 ga Watan Nuwamban 2019, wajen taron da kungiyar kolin addinin Musulunci, NSCIA, ta shirya.

KU KARANTA: Masu satar mutane za su rika mutuwa a kurkuku - Tinubu ta kawo kudiri

Mai dakin shugaban kasar ta tattauna ne a game da abin da ya shafi Musulunci da cigaban kasa. Aisha Buhari ta kuma soki gwamnoni na kin samar da abubuwan more rayuwa a cikin jihohinsu.

Aisha Buhari ta ce: “Dole mu gyara damararmu, mu yi abin da ya kamata, ko kuma duk mu dawo mu na da-na-sani, domin a yadda ake tafiya, abubuwa su na neman sukurkuce mana gaba daya.”

"Mataimakin Shugaban kasa (Yemi Osinbajo) ya na nan, wasu Ministoci su na nan, ya kamata su yi duba halin da mu ke ciki. Wasu mutane ba su da ruwan sha, alhali mu na da gwamnoni.”

“Tun da wannan ce babbar majalisar zartarwa ta addinin Musulucni a Najeriya, ga masu sauraro, mu ji tsoron Allah, mu tuna cewa wata rana za mu yi bayanin ayyukan mu da Duniya.” Inji ta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel