Yadda jama'a ke tsangwamata tare da ba'a - Zahra Buhari

Yadda jama'a ke tsangwamata tare da ba'a - Zahra Buhari

'Yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Indimi, ta koka da yadda 'yan Najeriya ke caccakarta a kafafen sada zumuntar zamani duk lokacin da mahaifinta ya yanke wani hukunci. Ta ce, tana wa wadanda ke tsangwamarta a yanar gizo addu'a saboda tana son ta cigaba a rayuwa.

Zahra ta sanar da hakan ne a yanki na farko na "Ganawa da Zahra", wani taro da gidauniyarta ta shirya a Abuja.

Taron da kudin shigarsa N10,000 ne ya jawo hankulan matasa masu tarin yawa.

A yayin bayyana yadda mutane ke tsangwamarta a yanar gizo da yadda ta samu kwarin guiwa, Zahra tayi mamakin dalilin da yasa mutane ke caccakarta tare da yi mata ba'a duk da cewa ba ita bace a kujerar mahaifinta.

A yayin bada labarinta tace, "A 2015 ne lokacin da na fara sanin mene ne tsangwama. Ya fara ne ta yadda hotona ya bazu. Ina wani atisaye ne kuma ina ta zufa. Amma mutane sai suka dinga turawa don cikar bukatar su a wajen yakin neman zabe.

DUBA WANNAN: Ina son zama 'yar kasuwa kamar Dangote - Jaruma Sadiya Kabala

"Amma kuma abun ya yi amfani ta wani bangaren. Mutane sun gano cewa 'yan arewa na da ilimi kuma mun iya turanci. Toh hakan ya canza kallon da wasu mutane ke yiwa 'yan Arewa na jahilci.

"An kammala zaben 2015 lafiya kalau. Bayan kwanaki 100, sai aka fara mita. 'Zahra mahaifinki yayi kaza da kaza. Amma ni ce a kujerar tare dashi? Ina yanke wani hukunci ne mai amfani?

"Kun san dalilin wasu hukunce-hukunce? Idan na saka hotona, hotona ne ba na danka ba. Ina mamakin yadda mutane ke nin haka akai-akai."

Ta bukaci wadanda ake tsangwama a yanar gizo da kada su damu da makiya. Ta kara da cewa, duk kalaman kiyayyar da ake musu cikin hassada ce.

Zahra ta kara da cewa, "Nasan akwai mutanen da hakan ke faruwa dasu a nan. Amma idan kana ciki, kamata ya yi ka tausayawa masu tsangwamarka. Suna fatan zuwa matakin da ka kai ne, amma suka kasa. Toh sai su yi kokarin jawo ka kasa. Zaka barsu ne? A'a. Yakamata ka san kana da wasu nagarta ne da mutane ke so."

Akan dokar daidaita kafafen sada zumuntar zamani da ke gaban majalisa a yanzu, Zahra tace tana goyon bayan daidaita kafafen soshiyal midiya din. "Amma yakamata mu gani tare da fahimtar abinda dokar ta kunsa."

Ta kara da cewa, "Ko dai mene ne, akwai bukatar mu fahimta tare da sanin abinda dokar ta kunsa. Abinda yakamata mu matasa mu yi kenan. Mu san meke faruwa a maimakon mu dinga tsokacin ba'a a kai tare da tura laifin ga wasu mutane ba gaira ba dalili. Ina goyon bayan dokar amma ta adalci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel