Kwastam! EFCC ta kwace fasfotin wani mashahurin dan kasuwa a Najeriya

Kwastam! EFCC ta kwace fasfotin wani mashahurin dan kasuwa a Najeriya

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kwace fasfotin shugaban kamfanin jiragen sama na Air Peace, Allen Onyeama, har zuwa kammaluwar bincike a kan zargin badakalar makuden kudin da Amurka ke mishi, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ta kara da ruwaito cewa, an dakatar da tafiye-tafiyen dan kasuwar na wucin-gadi kafin kammaluwar binciken.

Onyeama da shugaban bangaren kudi na kamfaninshi, Ejiroghene Eghagha na fuskantar bincike bayan da EFCC ta samu koke daga cibiyar shari'a ta Amurka a kansu.

Cibiyoyi shida na Amurka ke duba lamarin, kamar yadda majiya ta sanar.

Gwamnatin kasar Amurka ta ce, wadanda ake zargin zasu fuskanci shari'a ne a kan damfarar banki, almundahanar kudade, sata da sauransu.

Tuni kuwa hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta shirya bincike a kan 'yan Najeriyan da aka lissafo da hannunsu wajen aika-aikar.

An ruwaito yadda Onyeama ya amsa tambayoyi daga kwamitin a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Ina son zama 'yar kasuwa kamar Dangote - Jaruma Sadiya Kabala

An gano cewa, makomar Onyeama da Eghagha ta rataya ne a yarjejeniyar shari'a da ke tsakanin Najeriya da Amurka. Yarjejeniyar kuwa ta aminta ne da cewa duk wanda ake zargi a daya daga cikin kasashen zai iya fuskantar shari'a a kowacce kasar.

Wata majiya daga EFCC ta ce, "Biyo bayan tattaunawarshi da ma'aikatanmu, ya zama dole a hanashi zuwa wata kasa saboda akwai bukatar mu dinga samunshi lokaci zuwa lokaci,

"Mun kwace fasfotinshi ne don samun nagartaccen bincike. Kuma a dai yanzu, ya ba wa rundunarmu hadin kai.

"A yayin tattaunawarmu, ya tsaya a cewa yana da gaskiya. Kuma muna samun cigaba mai yawa a binciken farkonmu".

A kan yuwuwar mika dan kasuwar ga Amurka, majiyar ta kara da cewa: "Wannan ya dogara be da yarjejeniyar da ke tsakanin Najeriya da Amurka. A yanzu bincike kawai muke yi.

"Mikashi ga Amurka kuwa ya rataya ne a wuyan ofishin ministan shari'a na Najeriya. Kada ku manta EFCC sai ta bincika lamarin, ta samu gamsassun bayanai sannan ta mika wanda ake zargi gaban kotu, kafin bukatar mikashi ga Amurka ta fara aiki.

"Gwamnatin Amurka ta san abinda yakamata ta yi tunda ta san yarjejeniyar. Mu dai muna taka rawarmu ne a matsayin hadin guiwa da cibiyoyin Amurka da abun ya shafa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel