Kogi: 'Yan siyasa 3 da suka katsewa Dino Melaye cikar burinsa na komawa majalisa

Kogi: 'Yan siyasa 3 da suka katsewa Dino Melaye cikar burinsa na komawa majalisa

Tsohon dan majalisar dattawa da ya taba wakiltar yankin Kogi ta Yamma a karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye ya sha kaye a sake zaben yankin da aka yi.

Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ne ya karba kujerar, wanda hakan ya mayar dashi zababben sanata mai wakiltar yankin.

An maimaita zaben ne bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana rashin kammaluwar maimaicin zaben ranar 16 ga watan Nuwamba 2019.

Smart Adeyemi ya samu kuri'u 80,118 inda Dino Melaye ke biye dashi da kuri'u 59,548.

Ga 'yan siyasan da suka taka rawar gani wajen tabbatar da Dino Melaye ya sha mugun kaye a hannun Smart Adeyemi.

1. Adams Oshiomhole: Wannan dan siyasan ya taka rawar gani wajen tabbaatar da an kada Dino a zaben.

Bayan da Oshiomhole ya haye karagar shugabancin jam'iyyar APC a ranar 23 ga watan Yuli 2018, rigima ta shanye jam'iyyar wacce ta sa Dino Melaye tare da wasu sanatoci 15 suka canza sheka zuwa PDP. Wannan canza shekar kuwa ta gwada rashin kwarewar siyasar shugaban APC din tare da zama barazana ga jam'iyyar a majakisar dattawan. Adams Oshiomhole ya ce, masu canza shekar zasu fuskanci hukunci daga mazabunsu.

An zargi Dino Melaye tare da sauran wadanda suka canza shekar da tagayyara mulkin shugaba Buhari kuma an shirya don nuna musu kurensu.

A wani rahoton kwanannan, Oshiomhole ya ce, "Duk sanatoci 16 da suka bi ayarin Bukola Saraki wajen canza sheka sun fuskanci hukunci daga jama'ar yankinsu. Ina tunanin Dino Melaye ne kadai yake shure-shure. Amma kuma Smart Adeyemi ya fi karfinsa." Wannan jawabin kuwa ya taka rawar gani wajen salwantar da burin Melaye na komawa majalisar.

2. Gwamna Yahaya Bello: Ya shirya tsaf don koyawa Dino Melaye darasi. Gwamnan Kogin da tsohon dan majalisar sun rabu dutse a hannun riga bayan da Melaye ya koma PDP. An zargi gwamna Yahaya da shirya faduwar Dino a zaben.

Sau da yawa a majalisar dattawan, Dino Melaye kan koka cewa jihar Kogi na da fatara da ta yi mata katutu. Hakan kuwa ya biyo bayan kin biyan albashi da gwamnan ya yi ne tare da watanda da dukiyar jihar.

DUBA WANNAN: Ra'ayin Aisha Buhari da na Sarkin Musulmi sun banbanta kan dokar soshiyal midiya

Hakan kuwa ya kawo babban kalubale ga tsohon dan majalisar a mafarkinsa na komawa zauren majalisar, don tuni mutanen yankinsa suka shirya tsaf don kiransa ya dawo daga aikensa da suka yi majalisar. Yunkurin kiransa gida ya fadi ne bayan da INEC ta gano cewa, koken ba daga mazabarsa take ba. Amma kuma majiya wacce ba a tantance ba, tace Yahaya Bello ne ya shirya hakan.

Akwai kuma zargi da ke nuna cewa, Yahaya Bello ya shirya taro na musamman ana saura kwanaki kadan a maimaita zaben, wanda hakan ya jawo faduwar tsohon sanatan.

3. Smart Adeyemi: Ya shirya komai don kawo karshen siyasar abokin hamayyarsa. Zababben sanatan ya wakilci yankin jihar Kogi ta yamma a majalisa ta 6 da 7 kafin Melaye ya maka shi da kasa a 2015.

Adeyemi ya fuskanci kaye na wucin-gadi a hannun Melaye a 2019 kafin kotun daukaka kara ta soke zaben a watan Oktoba 2019.

Smart Adeyemi yayi amfani da rinjayen APC a jihar Kogi don birne burin komawa majalisar da Melaye yake. Duk da kuwa dacin kayen da Adeyemi ya dandana a hannun Melaye, ya samu nasarar watsi da abokin hamayyarsa sakamakon goyon bayan Adams Oshiomhole da Gwamna Yahaya Bello da ya samu.

Adeyemi, wanda ya rike shugaban kamfen din Yahaya Bello a jihar, ya yi amfani da wannan rinjayen wajen shirya faduwar Dino Melaye.

Kawu Dino, kamar yadda ake kiransa, ya yi ikirarin zai bige Adeyemi warwas a zaben, amma sai dai kash, zababben sanatan ya yi amfani da rinjayen APC a jihar wajen shirya birne burin Melaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel