Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya fadi ba nauyi, INEC ta alanta Smart Adeyemi matsayin zakaran zabe

Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya fadi ba nauyi, INEC ta alanta Smart Adeyemi matsayin zakaran zabe

Hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta INEC ta alanta Sanata Smart Adeyemi matsayin wanda yayi nasara a zaben kujerar sanata mai wakiltan Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya.

Adeyemi na jam'iyyar All Progressives Congress APC ya lallasa abokin hamayyarsa inda ya samu jimillar kuri'u 88,373 kuma Dino Melaye na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya samu kuri'u 62,133.

Hakazalika Ambasada Rufus Aiyenigba na Social Democratic Party (SDP) ya zo na uku da kuri'u 659 yayinda John Olabode and Adeyemi Taiwo na African Democratic Congress ya zo na hudu.

Adeyemi ya samu nasara ne bayan zagayen zabe na biyu da ya gudana ranar Asabar, 30 ga Nuwamba, 2019 tunda ba'a samu zakara a zaben 16 ga Nuwamba ba sakamakon rikice-rikice.

Tuni dai Dino Melaye ya bayyana cewa ya yi imanin cewa al'ummarsa shi suka zaba amma an rigaya da murde zaben tun kan a fara zabe.

Ya lashi takobin yakan wannan sakamako a kotu ko da INEC ta sanar.

Yace: "Ina alfahari da al'ummar Kogi ta yamma. Kun zabe ni amma an rigaya da shirye sakamako. Za mu yaki wannan rashin gaskiyan har karshe. Sakamakon karya ko ina."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel