Soke dokar biyar tsaffin gwamnoni makudan kudi: Ka yi mana dai-dai - APC ta yabawa gwamna Matawalle

Soke dokar biyar tsaffin gwamnoni makudan kudi: Ka yi mana dai-dai - APC ta yabawa gwamna Matawalle

Jam'iyyar All Progressives Congress APC shiyar jihar Zamfara ta yabawa gwamnatin abokin hamayyarta, Mohammad Bello Matawalle, kan soke dokar baiwa tsaffin gwamnoni, mataimakansu, tsaffin kakakin majalisa da mataimakansu makudan kudi da sunan alawus.

Jam'iyyar ta laburta wannan ne ta bakin mataimakin shugaban yankin Zamfara ta tsakiya, Sani Gwamna.

Gwamna wanda yayi hira da manema labarai bayan ganawar jigogin jam'iyyar a Gusau, ya bukaci gwamnatin tayi amfani da kudaden wajen ayyukan jin dadin al'ummar jihar.

Kan lamarin tsaron jihar kuwa, Sani Gwamna ya bayyana cewa wasu yan siyasa na amfani da yan bindigan wajen cimma manufarsu ta siyasa.

DUBA NAN Boko Haram: Soji sun ceto Likita, Unguzoma, da wasu mutane 18 a Yobe

A ranar Laraba, Gwamnan jahar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya rattafa hannu kan kudurin haramta biyan tsofaffin gwamnonin jahar kudaden fansho inda suka lakume miliyoyi, da wannan sa hannu na gwamna kudurin ta zama doka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Gwamnan ya rattafa hannu a kan kudurin dokar ne a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba a ofishinsa dake fadar gwamnatin jahar Zamfara, daga cikin wadanda suka halarci taron rattafa hannun akwai kaakakin majalisar dokokin jahar da dai sauransu.

Idan za’a tuna, a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba ne gwamnatin jahar Zamfara ta soke dokar da ta tilasta ma gwamnatin jahar Zamfara biyan tsofaffin gwamnoni miliyoyin kudade a matsayin kudin fansho, tare da haramta biyan gaba daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel