Melaye vs Adeyemi: APC ta yi wa PDP fintinkau a sakamakon kananan hukumomi 4 cikin 7

Melaye vs Adeyemi: APC ta yi wa PDP fintinkau a sakamakon kananan hukumomi 4 cikin 7

Smart Adeyemi, dan takarar jam'iyyar APC a zaben kujerar sanatar mazabar Kogi ta yamma yana gaba da Dino Melaye na jam'iyyar PDP a sakamakon kananan hukumomi hudu cikin bakwai da aka fitar kawo yanzu.

Yayin da Adeyemi ya samu kuri'u 5,609 a kananan hukumomi hudun, Melaye ya na da kuri'u 1882 hakan na nuna akwai banbancin kuri'u 3,727 tsakaninsu.

A karamar hukumar Lokoja, Adeyemi ya samu kuri'u 4,659, Dino kuma ya samu 920. A Mopa Morou, dan takarar na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 309 yayin da abokin karawarsa na PDP ya samu kuri'u tara tak.

Duk da cewa Melaye ya samu rinjaye da kuri'u kalilan a Koton Karfe da Ijumu inda 'yan takarar biyu suka fito, kayen da ya sha a kananan hukumomi biyu sun yi masa illa a zaben. Melaye ya samu kuri'u 376 a karamar hukumar Koton Kafe yayin da Adeyemi ya samu kuri'u 287.

DUBA WANNAN: Abinda yasa ba zamu amince da hukunci kisa ga masu satar kudin kasa ba - Majalisa Dattawa

A Ijumu, dan takarar na PDP ya samu kuri'u 577 yayin da abokin karawarsa na APC ya samu kuri'u 364.

A halin yanzu ana jiran sakamakon sauran kananan hukumomin a lokacin hada wannan rahoton.

Hukumar zabe INEC ta bayyana zaben ranar 16 ga watan Nuwamba a matsayin wanda bai kammalu ba wato (inconclusive) kasancewar kuri'un da aka soke sunfi yawan wadanda wanda ke kan gaba ya bada tazara.

Adeyemi ya samu jimla kuri'u 80,118 yayin da Melaye ya samu kuri'u 59,548. Hakan na nuna akwai tazarar 20,570 yayinda aka soke kuri'u 43,127.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel