Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta sake kama wa da wuta a Legas

Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta sake kama wa da wuta a Legas

Hukumar bayar ta agajin gaggawa na jihar Legas ta ce tanka dauke da man fetur lita 33,000 mai lamba KJA-900XR, a ranar Asabar ta kama da wuta a kan gadar Otedola da ke jihar.

The Punch ta ruwaito cewa mai magana da yawun hukumar LASEMA, Mista Nusa Okunbor ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas.

A cewarsa, binciken da aka gudanar ya nuna cewa tayar motar ne ya fashe yayin da ta ke tafiya.

Okunbor ya ce, "Tayoyin tankan ne suka kama da wuta saboda sakamakon zafi da ya taru saboda tafiyar da tankar ke yi.

DUBA WANNAN: Ra'ayin Aisha Buhari da na Sarkin Musulmi sun banbanta kan dokar soshiyal midiya

"An kashe wutan. Kuma babu wanda ya rasa ransa.

"Hukumar kwana-kwana ta Legas, LASEMA da Tiger Team suna nan a wurin domin kare afkuwar wani hatsari sakamakon gobarar motan."

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa wata tankar man ta kone a gadar ta Otedola a Yunin 2018 inda ta yi sanadiyar rasuwar mutane da asarar dukiyoyi masu yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel