Tun kafin a sanar da sakamako, Dino Melaye ya hakura

Tun kafin a sanar da sakamako, Dino Melaye ya hakura

Sanata Dino Melaye ya yi zargin cewa ana murde sakamakon karashen zaben kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma da hukumar shirya zabe mai zaman kanta wato INEC ke gudanarwa a yanzu haka.

Da alamun Dino Melaye, dan takara karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya kusa taba kasa dubi da irin sakamakon da ke fitowa daga yankin Kogi ta yamma.

Tun kafin hukumar INEC ta sanar da sakamakon, Dino ya bayyana cewa ya yi imanin cewa al'ummarsa shi suka zaba amma an rigaya da murde zaben tun kan a fara zabe.

Ya lashi takobin yakan wannan sakamako a kotu ko da INEC ta sanar.

Yace: "Ina alfahari da al'ummar Kogi ta yamma. Kun zabe ni amma an rigaya da shirye sakamako. Za mu yaki wannan rashin gaskiyan har karshe. Sakamakon karya ko ina."

A yau ake tsageta tsakanin Sanata Dino Melaye na jam'iyyar PDP da Sanata Smart Adeyemi na jam'iyyar APC a zaben kujerar majalisar dattawa na wakiltar mazabar Kogi ta yamma.

Kwamishanonin hukumar sun zanna ranar Alhamis sun tattauna kan lamarin zaben kuma sun yanke cewa ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba, 2019 za'a karasa zaben.

An soke zabe a akwatuna har 53 da ke cikin rumfunan zabe 20 da ke fadin yankin Yammacin jihar Kogi a zaben karshen makon jiya. Wannan ya sa aka kashe kuri’u 43, 127 inji hukumar INEC.

Smart Adeyemi ya lashe kuri’a 80, 118 ne yayin da Dino Malaye na jam’iyyar hamayya ya tashi da 59, 548. Tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takarar na 20, 570 bai kai 43, 127 da aka soke ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel